Fityanu za ta ƙaddamar da asusun taimakon marayu

0
532

Ƙungiyar addinin Musulunci ta Fityanul Islam ta Nijeriya ta bayyana cewa za ta samar wa dubban marayun da hare-haren ta’addanci su ka raba su da iyayen su a faɗin ƙasar nan matsuguni.

Ƙungiyar ta ce saboda haka ne ma za ta ƙaddamar da wani asusu na musamman a ranar Alhamis, 15 ga Disamba, 2022 domin gina Gidan Marayu na Sheikh Ibrahim Inyass da vibiyar koyar da Slsana’o’i a zariya, a Jihar Kaduna.

A sanarwar da mataimakin babban sakataran ƙungiyar ya rattabawa hannu, wanda kuma shi ne shugaban babban kwamitin shirya taron na ƙasa, Dakta Musa Muhammad Imam, ya ce za a yi ƙaddamarwar ne a lokacin babban taron ƙungiyar na shekara-shekara wanda za a gudanar a ɗakin taro na hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC) da ke Maitama, Abuja.

Ya ce haka kuma za a gudanar da zaɓen shugabannin ƙungiyar na ƙasa a washegarin ranar taron.Dakta Imam ya ce babban baƙo na musamman shi ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yayin da mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Kashim Shettima zai kasance shugaban taron.

Mataimakin babban sakataren ya ce babban mai ƙaddamarwa shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, sannan babban baƙo mai jawabi shi ne Babban Limamin Masallacin Ƙasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari.

Sheikh Muhammad Al-Arabi Sheikh Abdulfat’hi
Shugaban Fityanul Islam na ƙasa

Ya ƙara da cewa uban taron shi ne Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, yayin da iyayen taro su ne Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da Sheikh Shariff Ibrahim Saleh.

Sanarwar ta ce babban mai masaukin baƙi shi ne Ministan Gundumar Birnin Tarayya, Alhaji Muhammad Musa Bello, yayin da Sanata Abu Ibrahim da ɗan takarar gwamna na APC a Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, za su kasance masu taimaka masa.

Sheikh Muhammad Al-Arabi Sheikh Abdulfat’hi,National President of Fityanul Islam

Dakta Imam ya yi fatan ɗaukacin Musulmi za su yi ƙoƙari su halarci taron domin fa’idar sa.An kafa ƙungiyar Fityanul Islam ta Nijeriya (FIN) ne a shekarar 1962 a Kano a ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Inyass Al-Kaulahi, kuma tun daga wannan lokacin ta kasance mai taka muhimmiyar rawa wajen da’awar addinin Musulunci ta hanyar ɗaruruwan makarantun ta da ke cikin Nijeriya da sauran ƙasashen yankin Afrika ta Yamma.

Haka kuma ta kan yi aikin yaɗa koyarwar Annabi Muhammadu (s.a.w.), wanda ya haɗa da zaman lafiya da juna, da tsare dokokin addini da kuma neman ilimin addinin Islama.

Leave a Reply