Firaiministan Nijar ya soki ƙungiyar ECOWAS kan yin “zagon ƙasa” a yunƙurin samun mafita a rikicin ƙasar bayan wakilanta sun ƙaurace wa taron da ya kamata su halarta a ƙasar ranar Alhamis.
“Yau, baya ga Togo da ta yarda ta zo wannan taro, abin takaici shi ne ECOWAS ba ta zo ba,” in ji Ali Mahaman Lamine Zeine a wani taron manema labarai da ya gudanar a Yamai, wanda Ministan Harkokin Wajen Togo Robert Dussey ya halarta.
“Akwai masu yin zagon ƙasa a cikin wannan ƙungiyar watakila ma har da wasu ƙasashe da ke cikinta,” a cewar Zeine a yayin da Dussey ya ki cewa uffan.
An tsara taron ne domin Nijar ta tattauna da wakilan ECOWAS kan yadda za a samu mafita game da takunkuman da ƙungiyar ta kakaɓa wa ƙasar bayan sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.
KU KUMA KARANTA: Iran ta ce a shirye take ta taimakawa jamhuriyar Nijar, don shawo kan takunkuman da aka ƙaƙaba mata
Sojojin Nijar sun gayyaci wakilan ƙungiyar zuwa babban birnin ƙasar amma wakilin Togo ne kawai ya je.
Dussey ya je Yamai a watan jiya inda ya tattauna kan wa’adin mika mulkin kasar ga gwamnatin farar-hula kuma an tsara zai koma kasar tare da sauran wakilan ECOWAS da suka haɗa da takwaransa na ƙasar Saliyo Timothy Kabba.
“An sanya wa Nijar takunkumai ne domin a yi mata rashin adalci kuma babu wata doka da ta yarda da hakan. Mun yi bakin ƙoƙarinmu domin yin sulhu da su amma abin takaici sun ƙi amincewa,” in ji Zeine.