FBI ta Amurka, ta cafke wani ɗan Najeriya kan zargin damfarar dala miliyan 6 ta Intanet

0
26
FBI ta Amurka, ta cafke wani ɗan Najeriya kan zargin damfarar dala miliyan 6 ta Intanet

FBI ta Amurka, ta cafke wani ɗan Najeriya kan zargin damfarar dala miliyan 6 ta Intanet

Ana zargin Kayode wanda ya jima a jerin sunayen mutanen da hukumar, FBI, mai yaki da manyan laifuffuka a Amurka ke nema ruwa a jallo, da hannu a badakalar yin zamba ta hanyar amfani da sakonnin emel na kasuwanci (BEC) daga watan Janairun 2015 zuwa Satumban 2016.

Alkalin Alkalan Amurka, Susan Lehr ta sanar da tasa keyar Abiola Kayode, mai shekaru 37, daga kasar Ghana zuwa gundumar Nebraska, ta Amurka kan zargin samunsa da hannu a zambar dala miliyan 6 ta intanet.

A cewar sanarwar da ofishin alkalin alkalan Amurkan ya fitar a gundumar Nebraska a jiya Alhamis, ana zargin Kayode wanda ya jima a jerin sunayen mutanen da hukumar, FBI, mai yaki da manyan laifuffuka a Amurka ke nema ruwa a jallo, da hannu a badakalar yin zamba ta hanyar amfani da sakonnin emel na kasuwanci (BEC) daga watan Janairun 2015 zuwa Satumban 2016.

KU KUMA KARANTA:Wani matashi a Kano ya kai wa ‘yan sanda kuɗin da ya tsinta

Ta hanyar amfani da nau’in damfara BEC an zambaci ‘yan kasuwa a gundumar Nebraska dama wasu wuraren fiye da dala miliyan 6. An shigar da wannan korafi ne a watan Agustan 2019 a garin Omaha, dake Nebraska.

Leave a Reply