Farfesa ma fi ƙarancin shekaru a Yobe, ta farko da ta kammala digiri a jami’ar Harvard
Farfesa Hadiza Hamma farfesace a fannin shari’ar raya muhalli a tsangayar Shari’a ta jami’ar Abuja.
Ta fuskanci ƙalubale da dama kafin ta kai wannan matakin nata, ka ɗan daga cikin ƙalubalen da ta fuskanta shi ne ana buƙatar ta rubuta takardu da yawa kuma ta yi wallafe-wallafe da yawa sannan dole za ta halarci ɗalibai sannan dole ta je ɗakunan lakca, sannan ga kula da gida da iyali.
KU KUMA KARANTA:Ma’aikatar Ilimi ta jihar Yobe ta ba da lasisi ga makarantu masu zaman kansu
Ta ƙara da cewa ta shawo kan wannan ƙalubalen ne ta hanyar yin lissafin fifiko wanda shi ne abin farko don daidaita ma’auni kuma ta bi ta hanyar addini. Sannan ta horar da kanta wajen yin komai akan lokaci, sannan tana sauraron masu ba ta shawara da sauraron waɗanda suka ƙware a aikin.
Daga ƙarshe kuma tana mai bawa matasa mata shawara kan su jajirce su ci gaba da yin abin da suka yi imani da aikatawa su kasance masu ladabi da haƙuri dan ba za a iya komai ba ba tare da haƙuri ba.