Ƙungiyar ECOWAS ta cire takunkumin da ta saka wa Jamhuriyar Nijar wanda ya haɗa da batun rufe iyaka da kuma kasuwanci.
Ta bayyana haka ne a ranar Asabar a yayin taron da ta gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya. Haka kuma ƙungiyar ta sanar da janye takunkumin da ta saka wa ƙasar Guinea.
”Za a janye waɗannan takunkumai nan-take,” in ji shugaban majalisar ECOWAS Omar Alieu Touray bayan taron ƙungiyar.
Za a janye takunkuman da aka saka wa Nijar ne “bisa dalilai na jinƙai” domin sauƙaƙa wa ƴan ƙasar wahalhalun da suke sha, a cewar Touray a hira da manema labarai.
Ya ƙara da cewa: “Amma akwai takunkuman da aka sanya wa ɗaiɗaikun jama’a da kuma na siyasa waɗanda za su ci gaba da aiki.”
Tun a farkon watan nan ne Mali da Burkina Faso da Nijar suka sanar da ƙungiyar kan niyyarsu ta barin ƙungiyar, wanda wannan sabon lamari ne tun bayan kafa ƙungiyar a 1975.
KU KUMA KARANTA: Ɗaya daga cikin shugabannin da suka kafa ECOWAS ya nemi a cire wa Nijar takunkumi
Sai dai tun a jawabinsa na farkom Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa: “Dole ne mu sake nazari kan hanyar da muka ɗauka ta neman tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasashe mambobinsu,” in ji Tinubu.
“Saboda haka ina kira a gare su da su sake nazari dangane da matakinsu na ficewa daga gidansu haka kuma kada su ɗauki ƙungiyarmu a matsayin abokiyar gaba,” kamar yadda ya ƙara da cewa.
An shafe lokaci mai tsawo ana dambarwa tsakanin ECOWAS da Nijar da Burkina Faso da Mali, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce.