Dimokuraɗiyyar Turkiyya ta yi nasara a zaɓukan yankuna — Erdogan

0
122

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada muhimmancin dimokuraɗiyya da jajircewar ƴan kasa, ko yaya ta kaya a zaɓuka.

Da yake jawabi ga magoya bayansa a Ankara ranar Litinin da asuba jim kaɗan bayan an sanar da sakamakon zaɓukan magadan irane, Erdogan ya ce ƙasar Turkiyya ta yi amfani da zaɓe wurin aika saƙonta ga ƴan siyasa.

“Duk yadda sakamako ya kasance, babbar nasarar wannan zabe ita ce dimokuradiyyarmu, da kaunarmu ga kasa,” in ji Erdogan.

Ya miƙa godiya ta musamman ga mutanen da suka goyi bayan jam’iyyarsa da ƙawayenta, da kuma dukkan ƴan ƙasar da suka kaɗa ƙuri’unsu.

Da yake bayyana muhimmancin dimokuraɗiyya, Shugaba Erdogan ya jaddada goyon bayansa ga jajircewar ƴan kasar sannan ya ce koyaushe jam’iyyarsa tana bin tafarkin dimokuraɗiyya da tsarin zaɓe.

“Yau, mun gudanar da komai cikin tsari kuma ba mu yarda da komai ba idan ban da muradai na ƴan ƙasa,” a cewar Erdogan.

KU KUMA KARANTA: Turkiyya ta musanta zargin da ake mata na alaƙa da Isra’ila

Bayan Majalisar Ƙoli ta zaɓen ƙasar ta fitar da sakamakon zaɓen wucin-gadi, Shugaba Erdogan ya ce jam’iyyarsa za ta amince da sakamakon zaɓen.

“Ba za mu raina matakin da ƴan ƙasarmu suka ɗauka ba kuma ba za mu yi wa muradun ƙasarmu zagon-ƙasa ba,” in ji shi.

Shugaba Erdogan ya ce jam’iyyarsa ba za samu “sakamakon da take so ba daga zaɓukan yankuna da aka gudanar.”

“A jam’iyyance, za mu yi nazari game da sakamakon zaɓukan yankuna da aka gudanar kuma za mu yi wa kawunanmu faɗa.”

Leave a Reply