Dalilan da ya sa labaran ƙarya ya fi yaɗuwa – Dakta Hassan Gimba, a hirarsa da RFI Hausa

0
266

Daga Ibraheem El-Tafseer

Fitaccen marubucin nan kuma ɗan jarida, mawallafin jaridar Neptune Prime, Dakta Hassan Gimba ne ya bayyana haka a hirarsa da gidan Rediyon Faransa (RFI).

RFI HAUSA: Me ya sa labaran ƙarya ya fi yaɗuwa, musamman a kafafen yaɗa labarai na zamani?

DAKTA HASSAN GIMBA: Na farko kafafen yaɗa labarai na Afirka, ko dai na gwamnati ne ko kuma gwamnati tana da alaƙa da su. Don haka shi ya sa ba sa faɗin gaskiya a mafi yawan labaran da suke yaɗawa. Sannan wasu ‘yan jaridar ba su san makamar aiki ba (ba su da ƙwarewa a aikin jarida). Sannan akwai jahilci a wajen wasu masu sauraren, sun fi son labaran nishaɗi. Misali, yanzu a ce ga wani Gwamna yana fitsari a tsaye, to sai an fi tururuwar karanta wannan labarin akan idan ka ce ga wani Gwamna ya gina makarantu.

Su kansu waɗanda ake ƙira ‘yan jaridar, wasunsu ba wai sun ƙware bane a aikin jaridar. To yanzu Allah ya kawo mu wani zamani wadda da zarar mutum ya mallaki babbar waya, ya saka data, shikenan ya zama ɗan jarida. To sune waɗannan masu yaɗa labran ƙarya ɗin. Su kuma mutane sun fi son irin waɗannan labaran. Idan mutum ya rubuta labari na gaskiya, sai ka ga bai fi mutane 20 ko 40 ne suka karanta ba. Amma idan labarin ƙarya aka rubuta, sai ka ga mutane sama da dubu goma sun karanta.

KU KUMA KARANTA: Duk wani juyin mulki idan ya samu awa 24, to ya zaunu – Dakta Hassan Gimba a hirarsa da RFI Hausa

RFI HAUSA: Me ya sa ake yawan samun labarin juyin mulki a ƙasashen Afirka, alhali kuma ba gaskiya bane?

DAKTA HASSAN GIMBA: Su mutane suna ganin duk labaran da suke fito wa daga kafafen yaɗa labarai, ƙarye ne. Sannan kuma suna ganin duk labaran da ya fito daga wajen gwamnati ba gaskiya bane. Shi ya sa idan wani ya zo ya faɗi magana, sai a yi cincirindo a kanta, a ɗauka ita ce gaskiya. Ko irin juye-juyen mulki da ake a yi Afirka. Aka ce an yi a Gabon, sannan aka ce an yi a Kamaru, kuma mutane sun yi cincirindo, sun ɗauka gaskiya ne. Wannan kuma yana da alaƙa da halin ƙunci da ƙaƙa-ni-kayi da al’umma suke ciki.

RFI HAUSA: Kamar jama’a suna sha’awar irin waɗannan labaran ne ko kuma masu yaɗa labaran ne suka yi tasiri a kansu?

DAKTA HASSAN GIMBA: Abin da ya sa shi ne, kusan kowa ya zuba ido ya ga me zai faru a waɗannan wurare, saboda idan an yi juyin mulki a ƙasa kaza, saboda wasu dalilai. To saboda irin waɗannan dalilai, ya kamata a yi ƙasa kaza ma. Su kuma masu shafin yanar gizo, yawan masu bibiyar labaransu, waɗanda suke duba labaransu, a nan suke samun kuɗi da suna. To don haka, shi ya sa suke yaɗa irin waɗannan labaran.

RFI HAUSA: To waɗanne hanyoyi za a bi don daƙile irin waɗannan labaran?

DAKTA HASSAN GIMBA: To ka ga yanzu kamar ku RFI, BBC, DW, VOA da wasu kafafen yaɗa labarai na cikin gida suna iya ƙoƙarinsu. Amma waɗancan masu yaɗa labaran ƙaryar sun fi yawa. Sannan akwai wasu ƙungiyoyi, kamar a ce ‘Wole Soyinka Center For Investigating Journalism’ suna ƙoƙarin tallafa wa gidajen jaridu da gidajen Rediyo masu zaman kansu, domin su tsaya suna faɗin gaskiya.

Leave a Reply