Cutar sankarar Nono ba ta kisa muddin an yi gwaji da wuri: Wata ƙungiyar jin ƙai a Kamaru

0
65
Cutar sankarar Nono ba ta kisa muddin an yi gwaji da wuri: Wata ƙungiyar jin ƙai a Kamaru

Cutar sankarar Nono ba ta kisa muddin an yi gwaji da wuri: Wata ƙungiyar jin ƙai a Kamaru

Wani ayarin masu gudanar da ayyukan jin ƙai a Kamaru ya kai ziyara gida-gida a yankunan dake cikin ƙauyuka, domin bikin watan wayar da kai, kan cutar kansar mama, ko sankarar nono, inda suke ba wa mata shawara da su ziyarci asibitoci domin a yi musu gwaji kyauta, a kuma ba su magani.

Kimanin kashi 60% daga cikin 100 daga cikin sama da mata 7000 da aka samu dauke da cutar kansar mama a Kamaru sun mutu har lahira a bana, saboda rashin zuwa asibiti a kan lokaci, cewar jami’ai.

Wata daliba a fannin ilmin tarihi mai shekaru 30, Emilie Nadege Atangana, ta shaidawa wani gungun mata da yammata a jami’ar Yaounde, yadda ta shiga mummunan tashin hankali a lokacin da aka gano cewa, tana dauke da cutar kansar mama.

Tace, da dama daga cikin yan’uwanta, abokai da abokan karatun ta, sun juya mata baya tare da debe tsammanin cewa ba zata yi wani tsawon rai ba. tunda suka ji labarin cewa an gano tana da kansar nono a watan Yuli na shekarar 2020.

KU KUMA KARANTA:Uwargidan Shugaban Turkiyya ta ziyarci Najeriya don taron wayar da kai kan cutar kansa

Atangana tace ta fara samun karfin guiwar samun magani ne lokacin da likitocin cututtukan mata da na sauran cututtuka, na asibitin Yaounde su ka shaida mata cewa kashi casa’in daga cikin dari na sabon kamuwa da cutar kansar mama na iya warkewa sarai.

Jami’an gwamnatin Kamaru da kungiyoyin jin kai sunce an tura mutanen da suka warke daga cutar kansar nono, irin Atangana zuwa kauyuka da garuruwa a matsayin wani bangare na bikin watan wayar da kan mata game da cutar.

Hukumar lafiya ta duniya WHO tace, an kebe watan Oktoba a matsayin watan wayar da kan mata dangane da cutar ta sankarar nono ‘Pink Month’ domin sanar da mutane ilmi game da cutar, da ya hada da yadda za’a gane cutar tun da wuri da alamomin ta.

Ita ma Mesoke Ngwese Agbaw mai shekaru 42 a duniya da ta warke daga cutar sankarar nono, tana ilmantar da mutane domin su san cewa, ana warkewa daga cutar muddin aka gano ta da wuri. Tace bai kamata mutane su rika boye masu cutar a gida ba, a karshe har su mutu da tunanin cewa, ba’a warkewa daga cutar.

Leave a Reply