Cibiyar ƙwararru ta haraji ta karrama NIMASA

Hukumar kula da iyakokin ruwan Najeriya (NIMASA) ta samu lambar yabo na girmamawa daga cibiyar ƙwararru akan harkar haraji, inda shima Shugaban hukumar ya samu lambar yabo daga cibiyar a wajen taron liyafar cin abincin daren da ya gudana a birnin Legas.

A wata sanarwar da mataimakin darakta a sashin hulda da jama’a na hukumar, Mr Edward Osagie ya rabawa manema labarai yace hukumar NIMASA ta samu lambar yabon ne a ƙoƙarin ta na kiyaye dokokin da suka shafi biyan haraji da ayyukan jinƙai da hukumar ke yi a fadin Najeriya da kuma bada gudunmawar kayayyakin aiki da nufin inganta rayuwar masu ƙananan sana’o’in don habbaka tattalin arzikin Ƙasa.

A ɗaya bangaren, Shugaban hukumar ta NIMASA, Dokta Bashir Yusuf Jamo, ya samu lambar yabo ne a ƙoƙarin shi na tabbatar da ayyukan hukumar sun tafi daidai da na zamani.

KU KUMA KARANTA: Ana tsaka da Sallah ‘yan bindiga sun kashe Liman, sunyi garkuwa da masallata a Katsina

“Idan ba a manta ba, Bashir Yusuf Jamoh ya samu lambobin yabo da dama da suka hada da babbar lambar yabo ta ƙasa wato (OFR) wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya bashi a kwanankin baya,har ila yau, Dr Jamoh ya lashe lambar yabo a Shugabanci na Zik”.

“Ita da wannan lambar yabo da cibiyar kwararru akan harkar haraji ta baiwa Bashir Jamoh ita ce ta baya bayan nan a ƙoƙarin shi wajen ciyar da tattalin arzikin Nijeriya gaba” inji sanarwar.


Comments

3 responses to “Cibiyar ƙwararru ta haraji ta karrama NIMASA”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Cibiyar ƙwararru ta haraji ta karrama NIMASA […]

  2. […] KU KUMA KARANTA: Cibiyar ƙwararru ta haraji ta karrama NIMASA […]

  3. […] KU KUMA KARANTA: Cibiyar ƙwararru ta haraji ta karrama NIMASA […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *