Ana tsaka da Sallah ‘yan bindiga sun kashe Liman, sunyi garkuwa da masallata a Katsina

1
307

‘Yan ta’addan masu yin yadda sukeso a dajin Funtua ta jihar Katsina, a daren Asabar sun kai farmaki wani masallaci inda suka kwashe masu bauta waɗanda har yanzu ba a san yawansu ba.

Wani ganau ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a Maigamji dake ƙaramar hukumar Funtua ta jihar Katsina, AIT ta rahoto.Bincike ya nuna cewa, garin Maigamji yana kan babbar hanyar Funtua zuwa ƙaramar hukumar Ɗandume duk a jihar Katsina. A kan wannan babbar hanyar ne zata sada mai tafiya zuwa har ƙaramar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

An kai farmakin Ana tsaka da sallahKamar yadda ganau ɗin ya sanar, wurin ƙarfe 7:40 na dare yayin da Musulmi ke sallar Isha’i.Yace ‘yan ta’addan sun tsinkayi Masallacin inda sama da mutum 50 ke sallah, sannan suka fara harbi babu ƙakƙautawa kafin su yi awon gaba da mutane da ba a san yawansu ba.

KU KUMA KARANTA: Harin ‘yan bindiga a Masallaci ya jikkata mutane da dama a Delta

Sakamakon harbi, wasu jama’a sun samu raunika yayin da suke ƙoƙarin tserewa amma an gaggauta miƙa su asibiti.

Duk da ‘yan sanda ko wasu hukumomin tsaro dake jihar basu riga da sun tabbatar da faruwar lamarin ba, harin na zuwa ne bayan kwanaki ƙalilan da jam’iyyar APC mai mulki ta ƙaddamar da kamfen ɗin ta na 2023 na jihar a ƙaramar hukumar Faskari dake da makwabtaka da Funtua.Zagazola Makama a wallafarsu, sun sanar da cewa an halaka babban limamin Masallacin.

Duk da an bincika, har yanzu ba a tabbatar da yawan waɗanda lamarin ya ritsa dasu ba. An kuma sallaci gawar Liman kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.

Malam Sa’adu Faskari, wani matashi mazaunin garin Maigamji inda lamarin ya faru, ya sanar da cewa makwabcinsa yana daga cikin waɗanda lamarin ya ritsa dasu amma cikin karewar Ubangiji ba a tafi da shi ba.Sai dai ya samu raunika a ƙafafunsa har da guiwar hannu duk wurin ƙoƙarin tserewa.

“Al’amarin akwai matuƙar firgitarwa. Allah bai yi da ni lamarin zai faru ba don a Masallacin nake sallah. Sai dai nayi balaguro ne zuwa garin Dandume wanda kuma nayi dare sai na yanke hukuncin kwana a can.“Mummunan labarin ya riske ni inda na dawo da safe na samu jana’izar Liman.”

1 COMMENT

Leave a Reply