Binciken Jami’ar Oxford ya tabbatar allurar riga-kafin zazzaɓin cizon sauro data ƙirƙira na bada kariya, na tsawon shekara biyu

0
440

Gwaje-gwajen sabuwar allurar riga-kafin cutar zazzaɓin cizon sauro a yankin Afirka ta yamma da Jami’ar Oxford ta ƙirkira ya nuna riga-kafin na ba da kariya da kimanin kashi tamanin cikin 100 tsawon shekara biyu.

bayan da aka gwada riga-kafin a kan yara fiye da ɗari huɗu. Cutar zazzabin cizon sauro na halaka kusan yara miliyan ɗaya kowace shekara a yankin Kudu da Hamadar Sahara.

Tawagar masanan na Jami’ar Oxford tana aiki da cibiyar ta Serum da ke India wadda ke samar da allurar riga-kafin.

Farfesa Jenner da ke Jami’ar ta Oxford ta ce ”Abu ne mai kyau a samu amincewa saboda cuta ce mai wuyar samar da riga-kafinta.

Masu bincike sun ce za a iya samar da allurai kimanin miliyan ɗari cikin farashi mai sauƙi a shekara mai zuwa, a yayin da suke shirye-shiryen gabatar da bayanai ga Hukumar Lafiya ta Duniya nan da ƴan makwanni masu zuwa domin samun amincewarta.

Leave a Reply