Sarauniya Elizabeth mai shekaru 96, ta rasu bayan shafe shekaru 70 akan karagar mulki

0
272

Mai Martaba, Sarauniya Elizabeth, wacce ta fi daɗewa a kan sarautar Burtaniya, ta rasu tana da shekaru 96 bayan ta shafe shekaru 70 a kan karagar mulki.

Sanarwar da fadar Buckingham ta fitarce ta tabbatar da mutuwar ta. Sanarwar ta ce: “Sarauniya ta mutu cikin kwanciyar hankali a Balmoral da yammacin yau.

Sarki da Sarauniya Consort za su kasance a Balmoral a yammacin yau, kuma za su koma Landan gobe. ” Yarima Charles, Yariman Wales, ya zama Sarki kuma matarsa, Camilla, Duchess ta Cornwall yanzu ita ce Sarauniya.

Leave a Reply