Bikin Ista: Gwamna Buni ya ce ayi addu’ar zaman lafiya ga ƙasa

0
314

Gwamnan jihar Yobe Honorabul Mai Mala Buni CON,  ya yi ƙira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da bikin Ista wajen yin addu’o’in samun nasarar miƙa mulki cikin nasara da lumana, a daidai lokacin da Najeriya ke shirin sauya shugabanci.

Gwamna Buni ya bayyana hakan ne a cikin saƙon fatan alheri ga mabiya addinin Kirista a gudanar da bukukuwan Ista.

Ya ce, yana da matuƙar muhimmanci a sanya ɗabi’un son juna da sadaukarwa kamar yadda koyarwar Easter ke nunawa a wannan lokaci na rayuwarmu.

“Ya kamata a yi amfani da kyawawan darussan son juna da sadaukarwa don inganta zaman lafiya da haɗin kai don ci gaban ƙasa da ‘yan Najeriya,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: Bikin Sallah: Wata Cocin Kaduna Ta Raba kayan sawa, Kayan abinci Da Tsabar Kudi Ga Marayu Sama Da 50

Gwamnan ya bayyana cewa wannan lokaci ne mai albarka da mabiya addinin Kirista suka gudanar da bukukuwan Ista a daidai lokacin da ‘yan’uwansu musulmi ke gudanar da Azumin watan Ramadan.

“Don haka wata babbar dama ce gare mu a matsayinmu na al’umma da mu yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa ƙasarmu addu’a,” inji Gwamnan. Gwamnan ya yi kira ga shugabannin addini da na al’umma da su riƙa wa’azin zaman lafiya a kodayaushe.

“Zamu iya yin addininmu kuma mu samu wadata idan muka samu zaman lafiya. “A wasu shekarun baya, mun ka sa zuwa masallatai da coci-coci a jihar Yobe saboda ƙalubalen tsaro, amma a yau mun gode wa Allah da ya ba mu zaman lafiya a faɗin jihar.

“Don haka ya kamata mu kiyaye ta da husuma, mu guji duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da tsaro a jihar Yobe da Najeriya,” inji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here