Babu fargabar juyin mulki a ƙasar nan – Gwamnatin Najeriya

1
283

Gwamnatin Najeriya ta kawar da yiwuwar juyin mulki a ƙasar yayin da ƙasashen Afirka ke ci gaba da fuskantar hakan a baya-bayan nan.

Cikin wata hira da jaridar Punch ranar Juma’a, Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris ya ce ‘yan Najeriya sun gama rungumar dimokuraɗiyya.

“Ina tabbatar muku cewa babu wata fargaba kwatakwata. Mun wuce nan, saboda mun daɗe a cikin dimokuraɗiyya da kuma yadda ma’aikatu ke ƙara kafuwa a kan ta,” a cewar ministan.

Sau biyar aka taɓa yin juyin mulki a Najeriya tun bayan samun ‘yancin kai a 1960 – karo na ƙarshe da aka yi shi ne a 1993.

Ƙasar ta koma kan mulkin dimokuraɗiyya a 1999 bayan Janar Abdulsalami ya miƙa mulki ga farar hula, inda Olusegun Obasanjo ya lashe zaɓe a loakcin. Ana ci gaba da gudanar da zaɓen shugaban ƙasa duk shekara huɗu.

KU KUMA KARANTA: Da ɗumi-ɗumi: Sojoji sun yi juyin Mulki a ƙasar Gabon

Juyin mulki na ranar Laraba da aka yi a Gabon ne na baya-bayan nan a Afirka bayan wanda sojoji suka hamɓarar da gwamnati a Nijar ranar 26 ga watan Yuli a ƙasar mafi maƙwabtaka da Najeriya.

1 COMMENT

Leave a Reply