Ba za mu lamunci yunƙurin juyin mulki a Nijar ba – ECOWAS

2
367

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaba Bola Tinubu ya ce ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS) ba za ta amince da abubuwan da ke faruwa a Jamhuriyar Nijar ba.

Da safiyar yau Laraba ne rahotanni suka bayyana cewa dakarun tsaro sun toshe fadar shugaban ƙasa da ofisoshin jami’an gwamnati a ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Ba shiga ba fita a fadar shugaban ƙasar jamhuriyar Nijar, ana zargin yunƙurin juyin mulki

A martanin da ya mayar a cikin wata sanarwa, Tinubu wanda shi ne Shugaban ECOWAS ya ce ba za a lamunci yunƙurin juyin mulkin sojoji ba.

Sanarwar ta ce “Bayanan da aka samu daga jamhuriyar Nijar na nuni da wasu abubuwa marasa daɗi da ke faruwa a ɓangaren shugabannin siyasar ƙasar.”

2 COMMENTS

Leave a Reply