Asirin wasu matasa ya tonu lokacin da suka shirya aure akan sadakin wayar salula
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Asirin wasu matasa ya tonu, bayan da su ka shirya aure a bisa sharadin bayar da sadakin wata wayar salula da aka yi kiyasin kudinta akan naira dubu Arba’in.
Jami’an Hukumar Hisbah a karamar hukumar kura ne su ka kama matasan biyu, wadanda su ka hadar da Yusuf Akilu Hamisu, 30, wanda ya ke ikirarin shi ne Ango, da kuma Faroukh Lawan Yusuf, wanda ya ke a matsayin waliyin amarya.
Sai dai kuma abin al’ajabi, babu dangin iya babu na baba. Lokaci guda kurum su ka kirkiri auren domin ya zamar musu nishadi, kamar yadda amaryar gan-gan din Sadiya Isa Yar shekara 24, ta fadawa jami’an Hisbah tana mai cewar dukkaninsu mazauna unguwar Alkalawa ne da ke yankin karamar hukumar kura a Jihar Kano.
Sun dai gudanar da taron ne inda dakarun hukumar Hisbah su ka kai sumame wurin da ake sha’anin bayan wani bayanin sirri da su ka samu.
KU KUMA KARANTA:Hisbah a Kano ta rufe wasu shagunan da ake caca
Tuni shugaban Hukumar Hisbah a karamar Hukumar kura, Ustaz Ali Alkassim Kura ya sanar da al’amarin ga Shugaban karamar hukumar, Rabiu Abubakar Suleiman Babina, wanda ya bayar da umarnin gudanar da bincike don gurfanar da su a kotu.
Bayan an kammala bincike, an tasa keyarsu zuwa kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Garun Malam dake yankin karamar hukumar Kura.
Bayan da aka karanto musu laifukan da ake zarginsu da aikatawa sai su ka musanta.
Daga nan ne sai Alkalin kotun ya bayar da belinsu sannan ya dage ci gaba da zaman kotun.