Arziƙin Aliko Ɗangote ya haura zuwa dala biliyan 23.9

0
23
Arziƙin Aliko Ɗangote ya haura zuwa dala biliyan 23.9

Arziƙin Aliko Ɗangote ya haura zuwa dala biliyan 23.9

Alhaji Aliko Ɗangote, hamshaƙin ɗan kasuwa kuma shugaban rukunin kamfanonin Ɗangote, ya sake samun gagarumar nasara a duniya ta fuskar arziƙi.

A cewar mujallar Forbes, dukiyar Dangote ta kusan ninka sau biyu, inda ta kai dala biliyan $23.9, wanda ya sanya shi a matsayi na 86 cikin jerin attajiran duniya.

A baya can, dukiyarsa ta kasance dala biliyan $11.3, amma a watan Afrilu na shekarar 2024, an ruwaito cewa dukiyarsa ta kai dala biliyan $15.0, inda ya kama matsayi na 129 a jerin attajiran duniya. Wannan ci gaba na baya-bayan nan ya nuna irin gagarumin tasirin da babbar matatar man fetur da ya kaddamar ta yi a kansa.

Tasirin Matatar Man Fetur Ta Dangote

Ci gaban da Dangote ya samu ya biyo bayan kaddamar da babbar matatar man fetur ta Dangote, wadda ta kasance mafi girma a nahiyar Afirka. Bayan shekaru 11 na gini da zuba jari na dala biliyan $23, matatar ta fara aiki a shekarar da ta gabata. Tana da ikon sarrafa ganga 650,000 na danyen mai a kullum, wanda ya sanya ta zama ta bakwai mafi girma a duniya.

KU KUMA KARANTA:‘Yan kasuwa a Najeriya, sun ƙalubalanci Ɗangote da BUA kan hauhawar farashin Suga

Baya ga matatar man fetur, kamfanin Dangote yana da cibiyar samar da takin zamani mai karfin samar da tan miliyan 3 na urea a kowace shekara, wanda ita ma ta zama mafi girma a Afirka.

Rahotanni sun nuna cewa shigo da man fetur zuwa Najeriya ya ragu zuwa matakin da ba a taba gani ba cikin shekaru takwas, wanda hakan ya shafi masu tace mai na Turai da suka saba sayarwa Najeriya. Bugu da kari, Najeriya ta zama mai fitar da kayayyakin mai kamar su jet fuel, naphtha, da kuma fuel oil. Wannan ci gaba ya kawo sauyi mai ma’ana ga kasuwannin makamashi na duniya.

A wata hira da mujallar Forbes, Dangote ya bayyana cewa wannan matatar ita ce babbar jarumtar da ya taba yi a rayuwarsa. Ya ce,

“Idan wannan aikin bai yi nasara ba, da na lalace.”

Ya jaddada burinsa na ganin Najeriya ta zama kasa mai sarrafa albarkatun man fetur nata, domin ta iya gogayya da kasashen Turai wajen samar da man fetur ga ‘yan Najeriya.

Dr. Yusha’u Aliyu, mai sharhi kan tattalin arziki, ya bayyana wa Muryar Amurka cewa wannan nasara za ta iya samun tasiri mai yawa ga tattalin arzikin Najeriya. Ya ce, “Duba da irin girman hannun jarin da Dangote ya zuba da kokarinsa na bunkasa matatar, babu shakka hakan zai iya rage dogaro da shigo da man fetur daga kasashen waje.”

A cewar Dr. Yusha’u, matakin na Dangote na iya taimakawa wajen kara samar da ayyukan yi, rage radadin hauhawar farashin mai, da kuma bunkasa fannin masana’antu a Najeriya.

Tasirin Dangote A Najeriya Da Afirka

Wannan ci gaba ya kara tabbatar da matsayin Aliko Dangote a matsayin jagoran masana’antu a Afirka, tare da taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin Najeriya da ma nahiyar baki daya. Sai dai ‘yan Najeriya da dama na fatan wannan nasara ta Dangote za ta haifar da sauki a fannin sufuri da hada-hadar man fetur cikin kasa.

A cewar wasu masana, idan aka ci gaba da bunkasa matatar man fetur ta Dangote, hakan zai rage fitar kudi zuwa kasashen waje don shigo da man fetur, wanda a karshe zai iya taimakawa wajen bunkasa darajar Naira a kasuwar hada-hadar kudade ta duniya.

Alhaji Aliko Dangote, wanda ke ci gaba da zama mutum mafi arziki a Afirka, ya ci gaba da kafa tarihi ta fuskar kasuwanci da masana’antu, yana kuma nuna yadda jarumtar sa da hangen nesan sa ke kara daukaka Najeriya a idon duniya.

Leave a Reply