Muhawarar yankin da zai fidda dan takarar shugaban kasa tsakanin manyan jam’iyyu na APC da PDP na zama babban abun tattaunawa tsakanin manyan ‘yan siyasar Najeriya.
Yayin da akasarin ‘yan kudu ke cewa lalle dan takarar ya fito daga yankin su, ‘yan arewa na da bambancin ra’ayin abar takarar a bude kowa ya gwada karbuwar sa.
A zantawa da a ka yi da Shugaba Buhari da gidan talabijin na Channels ya nuna ba zai baiyana dan takarar da zai marawa baya ba don gudun kar a ma sa makarkashiya, da hakan ma ya nuna ba bukatar tambayar sa dan takarar na sa daga arewa ya ke ko kudu.
Ana raderadin irin su Bola Tinubu, Goodluck Jonathan da ma mataimakin shugaban Yemi Osinbajo ka iya zama a jerin wadanda a ke tsammani ke da tagomashi.
Ga babban dan siyasa Bamanga Tukur, barin takarar a bude shi ya fi dacewa da tsarin dimokradiyya.
A na sa bangaren tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, ya ce ba laifi in an ba wa kudu dama su fitar da dan takara, duk da ya na takaicin yanda ‘yan siyasar kudu ke zakewa cewa lallae lokacin su ne na shugabancin kasa.
A duk lokacin da gwamnoni ke ‘yan siyasar kudu ke magana na nuna mulki na su ne bayan kammala wa’adi biyu na Shugaba Buhari.
Nan ma tsohon ministan aiyuka ne Adeseye Ogunlewe ke cewa lokaci ya yi da arewa za su yi mu su kara su bar mu su tikiti.