An yi jana’izar marigayi Sarkin Tikau a fadarsa (Hotuna)

0
199

Daga Ibraheem El-Tafseer

Cikin hawaye da jimami aka yi jana’izar marigayi Sarkin Tikau, Alhaji Muhammad Abubakar Ibn Grema, wanda ya rasu ranar Juma’a, a fadarsa da ke Sabon Garin Nangere, Jihar Yobe.

Muhammad, wanda ya rasu yana da shekaru 73, an binne shi a inda aka binne sarakunan da suka gabata na masarautar Tikau.

Babban Limamin Masarautar Tikau Shaikh Adamu Mohammed ne ya jagoranci Sallar jana’izar a fadar da misalin karfe 4:15 na yamma kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, sakataren gwamnatin jihar, Baba Mallam Wali, kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Ciroma Buba Mashio, Sanata mai wakiltar Yobe ta Kudu (Zone B) Sanata Ibrahim Mohammed Bomoi, sarakunan Bade, Damaturu, Katagum, Kaltungo, Gujba, Machina, Jajere, Fune, Ngelzerma da sauran jiga-jigan gwamnati.

Ya rasu ya bar mata uku, ‘ya’ya 23 da jikoki da dama.

Masarautar Tikau na ɗaya daga cikin sarakuna 12 da aka ƙirƙiro a jihar Yobe, wanda marigayi Sanata Bukar Abba Ibrahim ya yi, bayan an ƙirƙiri jihar Yobe a shekarar 1991.

Ya gaji mahaifinsa marigayi Abubakar Grema a ranar 25 ga Yuli, 2001.

KU KUMA KARANTA: Sarkin Tikau na jihar Yobe ya rasu

Marigayi sarki, kafin zamansa Sarki, shi ne Principal na GSS Nangere kuma Hakimin Sabon Garin Nangere, daga nan kuma ya zama Sarkin Tikau. Ya yi mulki tsakanin 2001 zuwa 2024. Bayan zamansa Sarki, ya taɓa zama shugaban jami’ar jihar Yobe (chancellor).

Ɗaruruwan al’umma ne suka yi ɗafifi a fadar cikin cikin jimami da hawaye domin yiwa gawar sarkin bankwana.

Leave a Reply