An tsige Shugaban Masu Rinjaye da Mai Tsawatarwa na Majalisar Dokokin Jihar Jigawa.
Majalisar ta kuma dakatar da shugabannin ƙananan hukummi huɗu, bayan karɓar rahoton kwamitocin da ta kafa.
An tsige jagororin majalisar ne bayan samun su da laifin kitsawa da kuma goyon bayan yunkurin tsige shugaban majalisar a makonnnin da suka gabata.
Ɗan majalisa mai wakiltar Malam Madori, Hamza Ibrahim Adamu, ne ya gabatar da ƙudurin, wanda ya samu amincewar takwarorinsa.
Nan take bayan tsige Shugaban Masu Rinjaye, Hon. Aliyu Ahmed, mai wakiltar Kirikasamma da kuma Mai Tsawatarwa, Dayyabu Shehu Kwalo, mai wakiltar Taura, majalisar ta maye gurbinsu.
KU KUMA KARANTA: An bankaɗo sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba
Mambobin majalisar sun kuma dakatar da shugabannin kaknanan hukumomin Auyo, Dutse, Gumel, da Ringim, kan zargin badakalar kuɗaɗe.
Rahoton shugaban kwamitin kananan hukumomi na majalisar, Aminu Zakaria Tsibut, ya shida wa zauren mata cewa kwamitinsa ya gano badaƙalar kuɗaɗe a yayin aikinsa na sa ido a ƙananan hukumomi 27 na jihar.
Majalisar ta ce dakatar da shugabannin kananan hukumomin alama ce ta shirinta na bin diddigin kuɗaɗe da kuma yin komai a fili a matakin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi.