Ƴan sanda a Afirka ta Kudu sun ce sun kama fiye da mutum 130 a wani bincike da ake yi kan fyaɗen taron dangi da aka yi wa wasu mata a wani wajen haƙar ma’aidnai a gundumar Gauteng.
A baya ƴan sandan sun ce mutum 80 aka kama, amma sai aka ƙara kama wasu bayan nan.
An tare matan ne a yayin da suke naɗar bidiyon wata waƙa da suk yi.
Har yanzu ana ci gaba da yin bincike kuma ba a kai ga gurfanar da kowa kan zargin fyaɗe ba tukunna.
Mafi yawan waɗanda aka tsare ɗin sun sha gurfana a gaban kotu kan tuhume-tuhumen shige da fice, inda ake zargin su da shiga Afirka ta Kudu ba bisa ƙa’ida ba daga maƙwabciyarta Lesotho.
An yi wata zanga-zanga a Krugersdorp da ke yammacin birnin Johannesburg, inda lamarin ya faru, ana yin kira da a sake ɗaukar matakai kan hana haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba.