An kama da hodar ibilis sakaye cikin abincin jarirai a Legas

Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), a filin jirgin sama na Murtala Muhammed dake Ikeja a Legas sun kama wasu buhunan hodar ibilis da aka ɓoye a sassa daban-daban cikin kayan wani ɗan Najeriya da ya dawo daga ƙasar Brazil mai suna Nwadinobi Charles Uchemadu daga Sao Paulo,Brazil, inda ya biyo jirgin sama na Qatar ya shigo da shi Najeriya.

Uchemadu, wanda aka kama a filin jirgin sama na Legas

An kama Uchemadu ne a ranar Litinin 5 ga watan Disamba a filin jirgin sama na Legas, a lokacin da duba kayan fasinjoji shiga jirgin Qatar Airways sakamakon gano wasu buhunan hodar ibilis guda uku da aka rufe a sassan jakar tafiyarsa.

A wajen saukar jiragen sama na SAHCO a ranar, jami’an NDLEA sun kama gwangwanin madara, da abinci na jarirai da abubuwan sha da aka yi amfani da su wajen boye kilo 3.4 na tabar wiwi zuwa Dubai, An kama wani jami’in jigilar kaya, Ewelike Chibuike Cyril wanda ya gabatar da kayan, domin ya fitar zuwa kasashen ƙetare.

Hakazalika, a ranar Alhamis 8 ga watan Disamba, jami’an dai sun kama wani jami’in jigilar kaya, Joseph, sun kama wasu fakitin tabar wiwi masu nauyin kilogiram 6.30 da aka ɓoye a cikin na’urorin sauti (speaker) da ake ƙokarin fita da su Malabo, na ƙasar Equatorial Guinea ta tashar SAHCO da ke filin jirgin saman na Legas.

A ranar Juma’a 9 ga watan Disamba ne Obiji ya kama wani wakili, Mbanu Ifeanyi Andrew a wani samame da aka yi a kasuwar ASPAMDA da ke rukunin kasuwanci da ke unguwar Ojo a Legas.

A wurin da aka fi sani da Akala da ke unguwar Mushin a Legas, an kama wasu dillalan magunguna a kalla 15, ciki har da mata biyu dauke da kilogiram 1,400 na tabar wiwi da dai sauran haramtattun abubuwa kamar su tabar heroin, methamphetamine, da kwalabe 320 na maganin codeine da aka kwato daga hannunsu, a lokacin harin da aka kai yankin a ranar Juma’a 9 ga watan Disamba.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta yanke wa wasu ‘yan Ghana masu safarar wiwi zuwa Najeriya, hukuncin ɗaurin shekaru 72 a gidan yari

Wani samame da aka kai a unguwar da ke da hada hadar kasuwanci ta Idumota da ke cikin garin Legas a ranar Asabar 10 ga watan Disamba, a kama wasu ƙwayoyin Tramadol, diazepam, rohypnol da kuma lita 21.2 na maganin codeine guda 35,014 yayin da har yanzu ake neman wani ƙasurgumin dilallin ƙwayoyin ruwa a jallo.

Hakan na zuwa ne yayin da jami’an hukumar kula da ayyukan tashar jiragen ruwa na hukumar suka kama wani ɗan kasar Mali, mai suna Dembele Ousmane a ranar Litinin 5 ga watan Disamba dauke da kwalayen tramadol 32,400 na tramadol masu nauyin MG 225 da aka yi badda banin su cikin bokitin ajiyan kaya a lokacin da yake kokarin tafiya Mali ta jirgin ruwa a yankin Ebute -Ero a Legas.

A jihar Ondo, a ranar Talata 6 ga watan Disamba, jami’an ‘yan sanda sun kai farmaki dajin Ipele da ke unguwar Owo a jihar inda suka kama Rotimi Oyekan da Precious Aluju tare da C/S mai nauyin kilogiram 903.3, yayin da wata tawagar jami’an NDLEA suka kama Babatunde Oluyara a unguwar Igbotako. na jihar, tare da 168.5kgs na abu ɗaya; da wutsiyar biri mai nauyin 6kgs da nau’ikan methamphetamine, hodar iblis da tabar heroin.

A jihar Kebbi, an kama wasu mutane biyu Austine Julius da Sale Yakubu a ranar lahadi 4 ga watan Disamba a kan hanyar Yawuri zuwa Kebbi a cikin wata babbar mota, ɗauke da jakunkuna 117 na tabar wiwi mai nauyin kilo 1,070 a ɓoye a karkashin jakunkuna na lemu.

Kuma a ranar Litinin 5 ga Disamba, an kama wasu mutane biyu da ake zargi, Abdullahi Bala da Ibrahim Wade a kan hanyar Koko zuwa Kebbi a cikin wata babbar mota cike da jakunkuna 114 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 1,140 da aka ɓoye a karkashin akwatunan abubuwan sha.

Wani samame da aka kai a garin Abbi da ke karamar hukumar Ndokwa ta yamma a jihar Delta, ya kai ga kama wata mace mai ciki, mai suna Aniekem Evelyn ‘yar shekara 30 tare da kwato tabar wiwi mai nauyin kilo gram 1,161.

Yayin da yake yaba wa jami’an hukumar NDLEA da ke aiki a tashe jiragen sama ta MMI a Legas da Ondo, Delta da Kebbi bisa jajircewarsu da jajircewa da suka yi wajen kamawa da kwace kayayyakin a makon da ya gabata, Shugaban Hukumar, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (Mai Ritaya) ya buƙace su da sauran ‘yan uwansu da su ƙara ƙaimi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *