An jibge jami’an tsaro 40,000 a zaɓen gwamna a Kogi

0
153

Kimanin jami’an tsaro dubu 40 ne aka jibge a jihar Kogi domin tabbatar da an gudanar da zaɓen gwamnan jihar lafiya da za a yi a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.

Hukumomin tsaron dai sun sha alwashin tabbatar da tsaro a lokacin wannan zaɓe wanda ga bisa dukkan alamu yake cike da ƙalubale da kuma fargaba.

Zaɓen na jihar Kogi za a gudanar da shi ne tare da na jihohin Imo da Bayelsa da ke Kudancin ƙasar.

Jami’an tsaron da aka tura Kogin sun haɗa da sojoji da ‘yan sanda da kuma Civil Defence da ma sauran masu ɗamara tuni suka mamaye lungu da sako na jihar Kogin.

KU KUMA KARANTA: Za mu inganta tsaro ta hanyar haɗa kan jami’an tsaro da tattara bayanan sirri

Mataimakin Sufeto-Janar na ’yan sanda, DIG Habu Sani daga Hedikwatar rundunar ‘yan sandan  aka aika jihar ta Kogi domin tabbatar da zaɓen ya gudana lafiya.

DIG Sani ya kuma ce suna shirye da duk wasu masu tayar da zaune tsaye da ke shirin kawo cikas a lokacin zaɓen.

A halin da ake ciki dai Gwamna Yahaya Bello ya buƙaci rundunar ‘yan sandan Najeriyar da ta gudanar da kwakkwaran bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a rikice-rikicen da suka auku lokacin yaƙin neman wannan zaɓe na ranar Asabar.

Leave a Reply