An harbe shi har lahira a wurin gwajin maganin bindiga

An harbe wani mutum har lahira a lokacin da ake gwajin maganin bindiga da aka haɗa masa a jihar Bauchi.

Mutumin mai shekaru 43 da wasu mutum huɗu sun je daji Damaiwa ne domin a gwada maganin bindiga da wani mai tsubbu ya ba shi a ƙaramar hukumar Zaki a jihar.

Harba bindigar da bokan ya yi ke da wuya ta kama mutumin, wanda mazaunin ƙauyen Damaiwa da ke gudunumar Burasali ne, ya ce ga garinku nan.

Kakakin ’yan sandan Jihar Bauchi, Ahmed Wakil ya ce bayan samun labarin abin da ya faru ’yan sanda suka je wurin suka ɗauke gawar suka kai ta asibiti, inda likitoci suka tabbatar rai ya yi halinsa.

Ya tabbatar da cewa an kama mutum biyu daga cikin waɗanda aka je gwajin maganin bindigar da su, sauran ukun da suka tsere kuma ana neman su.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *