An gano ƙwarangwal din wata mata da ta buya a wani waje shekaru 4000

0
559

Daga Fatima MONJA, Abuja

Angano kwarangwal din matan ne da ake tsammani ta buya lokacin da ake girgizan kasa shekaru 4,000 a ƙasar Sin, wanda ta haifar da ambaliyan ruwa a sassa daban daban na ƙasar.

Cikin wani rahoto yan jaridan ƙasar sun ce masana kimiyyan sanin jikin dan Adam sun tabbatar da cewa ƙwarangwal din matar da kan yaronta sun shekara 4,000.

Sannan sunce ƙwarangwal din na uwace da ke ƙoƙarin kare yaronta daga babban girgizan ƙasan da ya faru a ƙasar Sin shekara ta 2000 BC.

A lokacin faruwar lamarin girgizan ƙasan, ta haifar da ambaliyan ruwa mai yawa da wasu lokuta ake kirada ‘China’s Pompeii’ kamar a gidan tarihin ƙasar Lajia Ruins Museum Chana ta bayyana.

Leave a Reply