An fara gudanar da taron ƙungiyar yaɗa labaran Afirka karo na 14 a Abuja

0
313

An samu mahalarta taron daga ƙasashen duniya daban-daban ciki har da Amurka. Taron zai duba abubuwa da dama kama daga gudumawar da kafafen yaɗa labarai su ke bayarwa wajen inganta cinikayya da ƙalubalen yaɗa shirye-shirye a yanayi na na’ura mai aiki da ƙwaƙwalwa da kuma dijital ko lataroni.

Taken taron na bana shi ne “Tasiri da ƙalubalen yaɗa labarun Afirka a cikin sauyin dijital na duniya”. Taro ne da gamayyar ƙungiyoyin yaɗa labarai a Afirka ta shirya tare da haɗin gwiwar hukumar Talabijin ta Najeriya wato NTA.

Wanan taro zai ba da dama a fahimci halayen kafofin yaɗa labaru na Afirka ta manyan batutuwan dijital da ke canja duniya. Hakan zai bai wa ‘yan kasuwa, manyan manajoji, malamai da masana damar yin aiki kan samar da arziƙi a ɓangaren yaɗa labarai.


A jawabinsa, Salihu Abdulhamid Dembos, shugaban Hukumar Talabijin ta ƙasa a Najeriya (NTA), ya yi bayani cewa kowace shekara ana gudanar da irin wannan taron wanda yake haɗa kan shugabannin gidajen yaɗa labarai na Talabijin da rediyo daga dukkannin sassan ƙasashen Afirka, inda sukan yi bitar ƙalubaloli da nasarorin da nahiyar Afirka ta ke samu ta fannonin yaɗa labarai.

KU KUMA KARANTA: Ranar ‘yan jarida ta ƙasa: Za mu bada goyon baya wajen yaɗa sahihancin labarai da kare ‘yancin ‘yan jarida – Kwamared Rajab

Abdulhamid ya ƙara da cewa, an samu koma baya a nahiyar Afirka ta fannin ƙirƙira, kuma saboda haka ne aka gayyato baƙi daga ƙasashen waje irin su nahiyar Turai, da Amurka, da ƙasar Rasha inda za su tattauna hanyoyin samun nasarori masu muhimmanci a nahiyar.

A nasa ɓangaren kuma, shugaban Hukumar da ke kula da kafafen yaɗa labarai ta ƙasar Najeriya Balarabe Shehu Ilella, ya yi nazarin taron inda ya ce yana da muhimmanci sosai domin za a yi ƙoƙarin canza yadda wasu ƙasashe suke kallon Afirka, domin a yanzu taron ya nuna cewa an ƙara samun zaman lafiya da haɗin kai a Nahiyar Afirka saɓanin yadda ake kallon nahiyar.
Balarabe ya ce nahiyar tana da ƙalubalen kayan aiki na zamani, saboda haka za a yi musayar ra’ayi wajen samun sabbin hanyoyin amfani da basirar ƙasashen da suka ci gaba.

Ɗaya daga cikin manyan baƙin da suka halarci taron kuma babbar darakta mai kula da sashin Afirka na Muryar Amurka Malama Salwa Jaafari ta bayyana farin cikin kasancewarta a wannan taron kuma ta ji daɗin gayyatar ta da aka yi. Salwa ta ce wannan wata dama ce da za ta haɗu da mutane daban-daban da suke da manufa iri ɗaya kuma masu wakilcin kafafen yaɗa labaru daban-daban daga ƙasashen duniya.

Salwa ta ce ta haɗu da mutanen da za ta iya hulɗa da su wajen yaɗa shirye-shiryen Muryar Amurka. Salwa ta ce abu na farko shi ne tattauna yadda ayyukan kafafen yaɗa labarai ke komawa na zamani. Ta ce wannan abu ne da zai zama mata abin alfahari da kuma jin daɗi ganin yadda ta samu karɓuwa wajen abokan aiki a Najeriya da na ƙasashen Afirka baki ɗaya.

Za a ci gaba da shirya irin wannan taron har ma za a shirya wani gagarumin baje kolin masu fasaha daban-daban daga sassa daban-daban na nahiyar a bainar baƙi na musamman.

Leave a Reply