An fara garkuwa da mutane ana sace musu ƙoda a Najeriya

0
70

Wani mummunan al’amari da ya ɓullo a Kaduna, yadda ake sace mutane ake cire musu ƙoda da ƙarfin tsiya, ba tare da suna so ba. Su waɗannan masu garkuwa da mutanen ba kuɗin fansa suke nema ba, ƙoda za su cire wa mutum, sai su sake shi. Suna da ƙwararrun likitoci da suke musu wannan aiki.

Akwai wata baiwar Allah da aka sace mata ‘yarta budurwa a Kaduna, ta shaidawa Neptune Prime cewa “‘yarta ta, ta samu matsala da bankin ta ne na rashin ganin ‘alert’, shi ne ta ce bari ta je a gyara mata matsalar a cikin bankin. Shikenan da ta fita ta hau Keke Napep zuwa bankin, ba ta farka ba sai cikin dare.

“Sai suka ɗauki wayarta suka ƙira gidansu suka shaida musu cewa sun sace ta ne, ba komai za su mata ba, ƙoda kawai za su cire su sake ta. Ana ta roƙonsu amma sun ƙi, sun ce wallahi sai sun cire.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Saman Najeriya ta halaka hatsabibin jagoran masu garkuwa da mutane, Janari, a Kaduna

“An yi waya da ita wadda aka ɗauka ɗin, mai suna Hafsa, tana ta kuka, tana cewa a yafe ta, don a kan idon ta an yiwa wasu ‘yan mata biyu tiyata ɗin, an cire musu ƙoda, amma ba su rayu ba, dukkansu sun mutu. Sai suka karɓe wayar suka shaida wa ‘yan’uwan ta cewa, ita aiki mai kyau za su mata. Ana ta roƙonsu ko kuɗi suke so za’a ba su, amma sun ƙi yarda. Sun ce lallai sai sun cire ƙodarta.”

Zuwa haɗa wannan rahoto babu ƙarin bayani a kanta. Da zarar an samu ƙarin bayani za a ji mu.

Leave a Reply