An cafke lauya kan lakaɗa wa matarsa duka

Wani lauya ya shiga hannun ’yan sanda kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan kawo wuƙa a Jihar Akwa Ibom.

A wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga Barista Sunday Ebong yana dukan matarsa, daga ita sai ’yar riga da ɗan kamfai a jikinta.

Kakakin ’yan sandan Jihar Akwa Ibom, SP Odiko MacDon, ya ce “an kama Barista Ekeere Sunday Ebong ne bisa zargin lakaɗa wa matarsa duka da aka baza a kofofin sada zumunta, inda aka ga ya ji mata rauni lokacin da yake dukan ta, ya farfasa mata jiki.”

Kazalika ana zargin Barista Sunday da kasancewa mutum mai yawan cin zarafin matarsa.

Wata ƙungiya Mai fafutukar ƙwato ’yancin mata ta sha alwashin bin shari’ar domin ganin an yi wa lauyan hukunci dai dai da abin da ya aikata.

KU KUMA KARANTA: ‘Dalilin da muka lakaɗa wa Alkali duka a Gombe’

SP MacDon ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar ya sha alwashin ganin an hukunta duk wanda ake zargi da cin zarafin iyalinsa ko na wani a jihar.

Rundunar ta ce ana ci gaba da binciken wanda ake zargi da yi wa matarsa dukan kawo wuka kuma da zarar an gama bincike kotu za a miƙa shi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *