An ɗaure ‘yan Najeriya 2 bayan damfarar wani ɗan Amurka da ya kashe kansa

0
111
An ɗaure ‘yan Najeriya 2 bayan damfarar wani ɗan Amurka da ya kashe kansa

 

An ɗaure ‘yan Najeriya 2 bayan damfarar wani ɗan Amurka da ya kashe kansa

Waɗanda suka zambatar sun haɗa da wani matashi ɗan shekara 17, Jordan Demay, daga jihar Michigan wanda ya hallaka kan sa da kansa.

An ɗaure ‘yan Najeriyar 2, wa da ƙani shekaru 17 da rabi a gidan kaso bayan da suka amsa laifin yin yaudara ta hanyar lalata a intanet da matasa maza a faɗin Amurka.

Waɗanda suka zambatar sun haɗa da wani matashi ɗan shekara 17, Jordan Demay, daga jihar Michigan wanda ya hallaka kansa da kansa.

KU KUMA KARANTA:Yadda ‘yan yahoo suka yi garkuwa da abokin ta’asarsu kan kuɗin damfara

A ranar Alhamis, wani alƙalin kotun tarayya ya yankewa Samuel Ogoshi mai shekaru 24 da kaninsa Samson Ogoshi dan shekara 21 hukunci bayan daya saurari bayanai masu ban tausayi daga iyaye da matar uban Jordan Demay.

Jordan Demay nada shekaru 17 da haihuwa sa’ilin daya hallaka kansa a gidansu dake garin marquette na jihar michigan.

Ana zargin ‘yan Najeriyar 2; Samuel da Samson Ogoshi da gudanar da wata kungiyar zambar-lalata ta kasa da kasa daga Najeriya ta hanyar gabatar da kansu a matsayin mata tare da zambatar wadanda suka fada hannunsu su aiko musu da hotunansu na batsa.

Bisa ga jami’ai, Samuel Ogoshi ya yi amfani da shafin sada zumunta mai suna dani.robertts a ranar 25 ga watan Maris 2022, bayan da suka rudi DeMay ya tura masu hotonshi tsirara, sannan ya yi masa barazana don ya biya toshiya.

A hirar ta da tashar talabijin ta TV6 mahaifiyar DeMay ta ce bata taba yin tsammanin hukumomi za su iya kamowa da kuma hukumta wadanda su ka yi sanadin mutuwar danta ba, ta ce, hukumomi sun yi daidai da suka tasa keyarsu zuwa Amurka domin amsa laifinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here