‘Yan bindiga suna ciyar da karnukansu da naman gawar mutane a Sakkwato — Malami

0
223
'Yan bindiga suna ciyar da karnukansu da naman gawar mutane a Sakkwato — Malami

‘Yan bindiga suna ciyar da karnukansu da naman gawar mutane a Sakkwato — Malami

Fitaccen Malamin addinin Musulunci a jihar Sokoto, Shaikh Bashar Ɗanfili, ya roƙi jama’a su taimaka musu da tallafin kuɗi bayan ‘yan bindiga sun yi garkuwa da ‘yan’uwansa.

Daily Trust ta rawaito cewa a wani gajeren faifen bidiyo da ya yaɗu a shafukan sada zumunta, Malamin ya ce mutanen da aka sace sun haɗa da wani mutum da mahaifiyarsa da kishiyarta da matasansa biyu da kuma ƙanwarsa.

Ya ce, ‘yan bindigar sun nemi kuɗaɗe masu yawa, wanda a yanzu sun kasa haɗawa, inda ya ƙara da cewa, wa’adin da ‘yan bindigar suka ba su na ƙara kusanto wa.

Malamin ya ce: “Yan bindiga sun sace makusanta na. Ba sai na fadi sunansu ba.

“Suna kan hanyar su ta zuwa wani kauye a yayin da aka kwashe su.

KU KUMA KARANTA:‘Yan bindiga a Sakkwato sun kashe ɗansanda da wani

“Sun kashe direban motar kuma suka baiwa karnunaka naman sa suka cinye.

” Sai dai ragowar mutanen har yanzu suna hannunsu, ciki har da miji da matan nasa da mahaifiyarsa.

“Yan bindigar sun bukaci miliyoyin kudade, wanda mun kasa hadawa.

” Ni Malami ne, bani da komai. Aiki na shi ne koyar da al’umma da littafan da kuke gani a baya na.

“Kuma sun bamu wa’adin lokacin da za a kai kudin, idan ba a kai ba zasu kashe su gabadaya.

” Nasan zasu iya yin hakan, duba da abinda ya faru da Sarki a kwanan nan.

“A don haka nake neman taimako daga al’umma domin biyan kudin fansa don sako su”.

Leave a Reply