Amurka ta ƙaddamar da shirye-shirye guda uku kan al’adu da ilimi a Najeriya

0
119

Mataimakiyar sakataren al’adu da ilimi a ma’aikatar harkokin wajen ƙasar Amurka, Lee Satterfield, ta bayyana haka ne a jami’ar Legas a ranar Laraba inda ta bayyana manufofin ƙasashen waje kan sabbin shirye-shiryen.

Ziyarar ta ta biyo bayan ganawar da Shugaban Amurka Joe Biden ya yi da shugabannin Afirka a birinin Washington DC a shekarar 2022 da kuma ziyarar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, wanda ya kai Najeriya a farkon watan Janairu.

Satterfield ta sanar da ƙaddamar da shirin African Creative Initiative a Talabijin, da shirin American Music Mentorship Programme ga waɗanda ke koyo a fannin ƙirƙire-ƙirƙiren, da kuma Community College, inda ɗalibai ‘yan Najeriya huɗu za su samu shiga kwalejin al’umma a Amurka.

KU KUMA KARANTA:Dakarunmu ba za su bar yankin Neja-Delta ba har sai an kamo waɗanda suka aikata kisan gillar – Rundunar Soji

Ta kuma sanar da ƙaddamar da wani fanni na samun bayannai akan jam’iyyun Amurka a UNILAG, inda ɗalibai za su iya samun shawarwari akan karatu a ƙasar da kuma hanyar samun shiga makarantun ƙasar da dai sauransu.

Satterfield ta ce, “Dawo wa ta nan yana da amfani don in yi magana game da faɗaɗa damammaki a tsakanin ƙasashen mu biyu a fannin ilimi da al’adu kuma na ambaci wasu sabbin tsare-tsare guda uku da muka ƙaddamar a yau; cewa akwai halin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa ta fanin ƙirƙire-ƙirƙiren. Muna ganin hakan zai ba da zarafin ƙaruwa da ci gaba saboda muhimmiyar rawa da hakan ya taka a faɗin duniya.

Satterfield ta kyautata zaton Shirin zai fara aiki a nan ba da jimawa ba a shekarar 2024.

Leave a Reply