Abarba na ɗaya daga cikin yayan itatuwa masu amfani a jikin ɗan Adam.
Abarba na da matukar amfani a jikin ɗan adam saboda tana ɗauke da muhimman abubuwa; fibres, menirals, vitamins, Nutrient da kuma Anti Oxidant.
Waɗannan sinadarai dai dake a cikin abarbar na da matukar amfani ga rayuwar ɗan adam, sannan takan kare jiki daga cututtuka.
Kaɗan daga amfanin abarba:
KU KUMA KARANTA: Anfanin ayaba 12 da ya haɗar da kiyaye lafiyar ƙoda, anfani ga mata masu juna biyu, da taimakawa ƙwaƙwalwar ɗalibai
- Tana ɗauke da sinadarin magnees da calcium wanda ke ƙara ƙarfin ƙashi
- Tana ɗauke da anti oxidant wanda ke ƙara ma jiki lafiya da kare jiki daga saurin tsufa.
- Tana maganin mura da sanyin ƙirji.
- Tana ƙara ma garkuwar jiki lafiya da kare shi daga cututtuka.
- Tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage cholesterol a jiki.
- Tana ƙara lafiyar dasashi da kare haƙora.
- Tana sauƙaƙa yawan laulayin ciki, da yawan amai da yawan tashin zuciya.
- Tana maganin tsutsar ciki.
- Tana ƙara ma idanu lafiya
- Tana ƙara lafiyar ciki da sauƙaƙa bahaya
- Tana maganin kumburi da maganin ciwon ga babuwa da fatan zamu rinka shan abarba akai akai.