Amfani Da Hoton Wani A Shafinka Na Sada Zumunta: Dacewa ko akasin haka?, daga Yusuf Alhaji Lawan

0
72
Amfani Da Hoton Wani A Shafinka Na Sada Zumunta: Dacewa ko akasin haka?, daga Yusuf Alhaji Lawan
Yusuf Alhaji Lawan

Amfani Da Hoton Wani A Shafinka Na Sada Zumunta: Dacewa ko akasin haka?, daga Yusuf Alhaji Lawan

Manyan maluma da sarakuna da ‘yan siyasa da sauran ma’abota girma a cikin al’umma, su ne aka fi amfani da hotunansu a shafukan sada zumunta na zamani a matsayin “profile picture”, a kuma shafukan da ba na su ba, kuma ba lallai da izininsu ba. Dalibai da mabiya da masoya da masu goyon baya sukan saka hotunan waɗannan muhimman mutane akan shafukansu musamman a ‘facebook’ da ‘whatsapp’ domin nuna ƙauna ko soyayya ko biyayya ko goyon baya a lokuta da dama.

Yana da muhimmanci mu fahimci cewa waɗannan muhimman mutane su ma mutane ne daban, waɗanda suke da zaɓi da tsari na rayuwa.

KU KUMA KARANTA: Meye ra’ayinka kan mauludi? Tattaunawarmu da wani a kan Mauludi, Daga Yusuf Alhaji Lawan

Sannan shi kuma mutumin da ya saka hoton, mutum ne na daban mai tunani da lissafi daban, wanda tsare-tsarensa na iya banbanta da nasu, musamman game da abubuwan da zai dinga sakawa a shafinsa, ba lallai ya zama ya wakilci tsarin wanda aka saka hotonsa ba.

Wannan ba zai zama daidai ba a tsarin tarbiyya da maslahar zamantakewa ta al’umma, ballantana a idon doka (hukuma). Idan abun ya ɓaci, zai iya kai wa ga ɗaukan matakin shari’a akan mutum ba tare da la’akari da girman abin da ya aikata ba.

Kuma yana da kyau mu fahimci cewa, a lokacin da muke amfani da hotunan malumammu ko sarakunanmu, da sauran shuwagabanni da hakan ke alaƙanta mu da su, ya zama tilas mu kula mu kuma kiyaye saboda makiya ma na iya amfani da hotunan domin yin wani abu na daban a shafukan sada zumunta don janyo musu suka ko Allah wadai ko ɓata suna a cikin al’umma.

Amfani da hoton wani don nuna soyayya ko ƙirƙirar goyon baya ba tare da izininsa ba, zai iya yin hanun riga da ra’ayinsa da tsarinsa, ko rage masa kima da daraja cikin al’umma ko jirkita iyaka tsakanin haƙiƙa da saɓanin hakan. Yana da kyau sosai idan za mu fahimci yiwuwar cutarwa dake tattare da amfani da hotunan wasu a shafukan da ba nasu ba.

Domin bayyanar da soyayya, ko biyayya da goyon baya ga wani a kafafen sada zumunta, mutum na iya saka hoton wanda yake so tare da bayanai dake nuna alaƙarsa da mai hoton ko bayyana goyon baya da makamancin haka.

A Najeriya, amfani da hoton wani dake nuna kamar shine a manhajar sada zumunta na iya zama laifi da za’a hukunta mai yin hakan a ƙarƙashin doka da aka kafa (Cyber Crime Prohibition and Prevention Act 2015) wacce kai tsaye ta haramta wani ya bayyanar da kansa a madadin wani.

A tanadin dokar an ce “duk wanda a cikin sani ko da niyya, ya aika saƙo ko abu makamancin haka ta hanyar na’ura mai kwakwalwa ko hanyar sadarwa wanda ya zama laifi, ko abubuwan da ke nuna tsiraici ko wani abu na rashin tarbiyya ko ɓata ɗabi’a” to yana daidai da a hukunta shi a gaban kuliya.

Hanya mafi sauƙi kuma mafi dacewa ita ce mutum ya yarda ya saka hotonsa ba na wani ba, akan shafukansa a manhajojin sada zumunta na zamani, ko kuma ya nemi hoton wani abu na daga dabbobi ko zane-zane ko furanni da sauransu da za su wakilce shi.

Wannan zai kiyaye mutum daga samun saɓani da wani, sannan kuma zai taimaka wa mutum wajen bayyana kansa ko ra’ayinsa ko abin da yake da sha’awa akai.

Lura da kiyaye ƙa’idoji na mu’amala a shafukan sada zumunta na zamani abu ne mai muhimmanci da zai tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya ga mutane da kuma kiyaye maslahar zamantakewa a tsakanin jama’a.

Wannan abu ne da ya shafi kowa kuma ya kamata duka mu haɗa kai wajen tafiya akan tsarin da zai zama mai amfani ga kowa da kowa.

Yusuf Alhaji Lawan ya rubuta daga anguwar Hausawa Asibiti, garin Potiskum jihar Yobe. Kuma za’a iya tuntuɓarsa ta nasidi30@gmail.com.

Leave a Reply