Ambaliyar ruwa ta haddasa asarar rayuka da lalata gidaje sama da100 a Gombe

0
242

Daga Fatima GIMBA, Abuja

Sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka yi a garin Bajoga da ke karamar hukumar Funakaye a jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya, ya haddasa mummunar ambaliyar ruwa.

Ambaliyar ruwan dai ta yi sanadin mutuwar wani yaro dan shekara uku tare da rusa gidaje aƙalla dari.

yadda ruwa ya maida garin

Kazalika, ambaliyar ta kuma janyo mutane da dama sun samu raunuka a inda a yanzu haka suke kwance asibiti suna karbar magani.

Da safiyar ranar Asabar din karshen watan Yuli ne aka maka ruwa a garin na Bajoga inda aka shafe kusan sa’oi biyar ana tafka ruwan lamarin da ya haddasa ambaliyar.

Wasu da lamarin ya faru a kan idanunsu sun shaida cewa ruwan ya kuma yi sanadin asarar dukiya mai yawan gaske ciki har da dabbobi.

KU KUMA KARANTA: SANARWA: Hasashen NIMET, NIHSA ya ja hankalin Jihar Yobe kan ambaliyar ruwa

Malam Ahmad Sulaiman, mazaunin garin Bajoga ne ya ce a yanzu a garin nasu wasu gidajen sun zamo tamkar kufai.

Ya ce, “Mutanen da wannan ambaliyar ruwa ta shafa a yanzu suna cikin wani hali, gidaje duk sun jiƙe babu wajen kwanciya, babu abin da jama’a ke bukata a wannan yanayi illa taimako.”

Malam Ahmad Sulaiman, ya ce da yawa daga cikin mazauna garin ruwa duk ya tafi da abubuwansu, baya ga asarar dabbobi.

Tuni dai gwamnatin  jihar ta Gombe ta ce tana nazarin hanyoyin da za ta taimaka wa al`ummar da iftila’in ambaliyar ruwan ya shafa.

Gwamnatin  ta ce a yanzu tana nazarin wani rahoto daga wani kwamitin da ta kafa, wanda ya je ya yi ƙididdigar girman masifar ambaliyar da ta afka wa al’ummmar unguwar Shahar Mansur da ke garin na Bajoga ya mika mata da nufin duba irin taimakon da ya kamata a yi wa wadanda iftila’in ya shafa.

Alhaji Isma’ila Uba Misilli, shi ne babban daraktan da ke kula da harkokin yada labarai na gidan gwamnatin jihar ya ce duk inda za ka ji an ce sama da gida 100 wannan al’amari ya shafa, to lallai babban abu ne wanda ba lallai gwamnatin jiha ce kadai za ta iya daukar nauyi ba.

Ya ce, da masu hannu da shuni da gwamnatin tarayya da ma dukkan hukumomin da ke bayar da agaji za a so a ce su ma sun shigo cikin lamarin.

Tuni dai wasu ƴan siyasa da daidaikun jama’a suka fara kai dauki ga mazauna unguwar ta Shahar Mansur, wadanda albaliyar ta tilasta musu gudun hijira.

Leave a Reply