Allah Ya yi wa ɗan Sarkin Zazzau rasuwa

0
76
Allah Ya yi wa ɗan Sarkin Zazzau rasuwa

Allah Ya yi wa ɗan Sarkin Zazzau rasuwa

Daga Idris Umar, Zariya

Allah Ya yi wa ɗan Isan Zazzau, Alhaji Umar Shehu Idirs, rasuwa a wani hatsarin mota da ya auku da yammacin ranar Talata.

Jami’in hulɗa da jama’a na masarautar Mallam Abdullahi Aliyu Kwarbai ne, ya tabbatar da rasuwar.

Kafin rasuwarsa, Umar Shehu Idris ya kasance Mataimakin Sakatare a Majalisar Masarautar Zazzau.

Ya rasu yana da shekara 41, ya bar mata biyu da yara biyu.

KU KUMA KARANTA: Allah Ya yi wa mahaifiyar tsohon shugaban ƙasa Yar’Adua rasuwa

Mahaifiyarsa ta kasance mata ga tsohon Sarkin Zazzau, Dakta Shehu Idris, kuma mahaifiyar matar Sarkin Zazzau na yanzu, Ahmed Nuhu Bamalli, wadda ta rasu kwana 39 da suka gabata

Dukkansu anyi masu kyawawan shaida tare da fatan samun rahamar Allah maɗaukakin sarki.

Leave a Reply