Akalla Mutane Miliyan 5 Su Ka Yi Azumi Na Musamman Domin Neman Daukin Ubangiji A Jihar Kaduna

0
590

Daga; Bashir Dollars, Kaduna.

A BISA yunkurin da su ke na ganin cewa an samu nasarar kawo karshen duk wata ukuba da halin kuncin rayuwa a Jihar Kaduna, akalla mutane sama da Miliyan biyar suka gudanar da Azumi na musamman a ciki da wajen Jihar domin neman daukin Ubangiji dangane da yanayin halin rayuwa da al’ummar Jihar su ke ciki.

Azumin wanda ya gudana a ranar litinin sakamakon wani kira da Dan takarar Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna, a karkashin Jam’iyyar APC, Honarabul Sani Sha’aban ya yi, an gudanar da taron bude baki na shan ruwan Azumin wanda ya samu halartar akalla sama da Fastoci 30 da wasu manyan malaman Addinin Musulunci a ofishin kamfen dan takarar dake garin Kaduna.

Da yake jawabi a wajen taron bude bakin Azumin, Dan takarar kuma Buran Zazzau Sani Sha’aban, ya bayyana cewa wannan wani mataki ne da suka dauka domin neman kawo karshen halin ha’ula’i da al’ummar Jihar ke ciki sakamakon irin yadda al’amura na rashin kwanciyar hankali suke kasancewa.

Ya kara da cewa al’ummar Jihar basu da wani karfi wanda ya wuci karfin Ubangiji kuma a dalilin hakan ne suka gudanar da wannan Azumin na musamman domin neman daukin Shi a cikin rayuwar su da al’amuran Jihar Kaduna wanda hakan ke neman salwantar da rayuwar al’ummar.

Ya ce “Ni mutumin Zariya ne kuma daga Zariya na Fito, kuma yanzu haka akalla sama da mutane Miliyan daya suka gudanar da wannan Azumin wanda mu ka yi bude baki a nan cikin cikin garin Kaduna.”

“Kuma ga duk wanda ke son tabbarwa, a nan cikin garin Kaduna akalla sama da mutane Miliyan daya suka gudanar wannan Azumin, haka a garin Zankuwa, Kafanchan da Kachia kuma muna saran Allah Zai dubi kokanmu ya jibanci al’amuran mu ta hanyar da zamu samu saukin rayuwa.

Acewarsa, wasu da dama daga cikin al’ummar Jihar sun rasa ayyukan su, a yayin da wasu matasa suka kasa yin karatu sakamakon karin kudin wanda hakan yasa iyayensu basa iya biyan kudin makarantarsu.

Dan takarar Kujerar Gwamnan, ya ci gaba da cewa akalla kusan kwanaki casa’in kenan da aka yi garkuwa da yan Uwansu wadanda suka hada da Sadiq Ango Abdullahi, MS Ustaz da sauransu a harin Jirgin Kasa, to amma har yanzu Gwamnatin ta kasa yin komai domin ganin an sako su.

Honarabul Sha’aban, ya kara da cewa ya shigar da kara kotu domin neman hakkin shi a bisa karfa-karfan da aka yi masa a lokacin zaben fidda gwani na Jam’iyyar ta APC, kana ya aika da sakon neman ita Uwar Jam’iyyar ta dauki matakin da ya dace na ganin cewa ta daidaita al’amura a tsakanin duka Ya’yan Jam’iyyar.

Hakazalika, ya yi nuni da cewa masu zaben yan takara mutane 1224 da suka sayi fom din zama masu zaben yan takara da a basu dama ba, su ma sun shigar da kara kotu domin neman hakkin su bisa rashin adalcin da aka yi musu da tauye musu hakki a lokacin zaben.

A karshe, Barden Keffi Sani Sha’aban, ya bayyana cewa suna saran wannan Azumin da suka gudanar kuma su kayi tawassali da ita, zata zame musu wata silla na samun waraka bisa duk wata damuwar da ta addabe su a ciki da wajen Jihar ta Kaduna.

Leave a Reply