Abincin da ake nomawa a arewacin Najeriya, ya isa a ciyar da mutanen ƙasar nan – Farfesa Abdulkarim

0
366

Daga Abubakar M Taheer

Shugaban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Dutse Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammad ya bayyana irin damarmakin da Arewacin ƙasar ke da shi wajen noma dama ciyar da al’umma ƙasar gaba.

Haka kuma ƙasar tana da hanyoyin kasuwancin kayan abincin tsakanin ƙasashen duniya.

Farfesa Abdulkarim ya bayyana haka ne a karon farko da Masana kimiyyar Abinci suka gabatar a Jami’ar Bayero dake Kano.

Taken taron na bana dai shi ne “Samarwa Abincin da ake nomawa a Arewacin Ƙasar nan wurin zama a Kasuwannin Duniya”.

Farfesa Abdulkarim Ya bayyana cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ake alfahari da ita a Afirka dama duniya baki ɗaya da Allah ya horewa ƙasar noma.

Farfesa ya bayyana irin yadda masana daga ko’ina a faɗin duniya suke gabatar da ƙasidun albarka noma da ƙasar take da shi kama daga noma Masara, Dawa, Gero, Maiwa da sauransu.

“Wanda da a ce shugabannin ƙasar nan za su haɗa hannu da masana, cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar za ta zama abun kwatance a duniya dama samun hanyoyin shigowar kuɗi ga ƙasar.

Ana ta jawabin shugaban ƙungiyar Masana Kimiyyar Abinci ta Arewa Maso Yamma, Dakta Zahra’u N Bamalli, ta bayyana cewa manufar wannan taron shi ne shigo da masana kimiyyar abinci daga ko’ina a faɗin Arewacin ƙasar nan domin haɓaka yankin gaba ɗaya.

KU KUMA KARANTA: WHO ta ce mutane miliyan 60 za su fuskanci matsalar abinci a Afirka

Dakta Zahra’u ta ƙara da cewa, tun asalin Arewacin Nijeriya na da tarin abinci wanda ake yin su tun iyaye da kakanni, wanda ya zama dole ga masana su rinƙa yin nazari dama fito da amfanin su domin ingantawa gami da gogayya da sauran taƙwarorinsu na duniya.

“Ya zame mana dole mu rinƙa inganta abinci gargajiya tare da shigo da dabarun alkinta yadda ake yinsu, domin kula da lafiya al’ummar dama kare su daga barazanar kamuwa da cututtuka wanda aka iya kamuwa ta hanyar rashin inganci abinci.

Idan ya zama an inganta abincin mu, aka shigo da dabaru zamani wajen yinsu, nan gaba kaɗan Arewacin ƙasar zai zama abin kwatance.

Dakta Zahra’u ta ƙara da cewa, “muna so irin wannan taron ya zama wata inuwa da za ta rinƙa haɗa, masu bincike, masana, shugabanni dama masu kamfanonin sarrafa abinci dake arewacin ƙasar nan.

Tunda farko ƙwararrun masana, daga sassa daban-daban sun gabatar da ƙasidu, haka kuma taron ya samu halartar ɗalibai daga cikin jami’o’in ƙasar nan.

Leave a Reply