Abin da ya sa aka ba da belin matar da ake zargi da kashe mijinta a Damaturu – Suleiman Hassan Gimba Esq

0
493
Abin da ya sa aka ba da belin matar da ake zargi da kashe mijinta a Damaturu - Suleiman Hassan Gimba Esq
Zainab Isa

Abin da ya sa aka ba da belin matar da ake zargi da kashe mijinta a Damaturu – Suleiman Hassan Gimba Esq

Ita wannan mata da ake zargi da kashe mijinta ta samu administrative bail through effort na FIDA.

Wannan zai ba da dama ga ‘yansanda su zurfafa bincike akan asalin abin da ya faru, ita kuma ta nemi kulawa ga lafiyarta.

Su kansu ‘yansandan sun tabbatar da cewa tana zubda jini ta wajen da aka yi mata tiyatan haihuwa (CS) a dalilin naushi a cikinta da mijin ya yi mata.

Zai yiyu ita ma victim ce na domestic violence a hannun mamacin.

Ko kuma a garin kare kansa da ta ɗauko wuƙa ya yi ta mata naushi.

Bincike ne kaɗai zai tabbatar da asalin abin da ya faru.

Shi yasa bai kamata a ce ana yiwa waɗanda ake zargi da aikata laifi video ana ɗaurawa ba tare da zurfafa bincike ba.

Duk aikataccen laifi yana da ɓangare biyu. Actus reus (shi asalin physical in) da kuma mens rea (shine halin da mind na mai aikata laifin yake ciki, za a iya cewa niyya ko rashinta).

KU KUMA KARANTA: Ƴan sanda a jihar Yobe sun kama wata mata da kashe mijinta da wuƙa

Ko daga videon da aka mata, za a iya cewa ba ta da niyyar aikata laifin kisa, kuma kare kanta take yi.

Sashi na 33(2) (a) na Constitution ya ce ba za a ɗauki mutum da ya mutu a irin halin wannan mamacin a matsayin wanda aka hana shi rayuwarsa ba in an yi amfani da gwargwadon ikon da shari’ah ta gamsu da shi don kare kowane mutum daga tashin hankali ba bisa ƙa’ida ba ko don kare dukiya.

Kuma Sashi na 286-293 na Criminal Code da Sashi na 59-67 na Penal Code sun ƙara jaddada bayanai akan kare kai.

Shi laifin kisa ya rabu kashi biyu ne;

Akwai Sashi na 221 Penal Code Culpable Homicide Punishable with Death (wanda akwai hukuncin kisa)

Da kuma Sashi na 222 Culpable Homicide not Punishable with Death (wanda ba hukuncin kisa.)

Duk waɗannan alƙali ne kaɗai zai iya amfani da duk hujjojin da ke gabansa da abubuwan da dokokin ƙasa suka ce sai ya auna, ya yanke hukunci yadda ya da ce.

Leave a Reply