Wani direba ya hallaka soja guda da jikkata da dama a Legas

0
30
Wani direba ya hallaka soja guda da jikkata da dama a Legas

Wani direba ya hallaka soja guda da jikkata da dama a Legas

Sashe na 81 na rundunar sojin Najeriya ya bayyana cewar direban wata motar gida ya bi ta kan wasu dakaru cikin ganganci yayin da suke tsaka da tattakin da suka saba yi sau 2 a shekara kusa da barikin Myhoung dake unguwar Yaba, ta jihar Legas, a yau Juma’a.

Hakan yayi sanadiyar mutuwar soja guda, tare da sabbabawa wasu da dama nau’ukan raunuka daban-daban, a cewar sanarwar da mai rikon mukamin mukaddashin daraktan hulda da jama’a na sashe na 81 na rundunar sojin Najeriya, Laftanar Kanar Olabisi Ayeni.

KU KUMA KARANTA:An halaka direba da sace mutum 2 a hanyar Abuja

Ya kara da cewa an ajiye gawar hafsan da ya mutun a dakin ajiyar gawa yayin da wadanda suka jikkatan ke samun kulawar likitoci a asibitin sojoji Najeriya na 68 dake unguwar Yaba, ta birnin Legas.

Laftanar Kanar Ayeni yace bangaren ‘yan sanda na rundunar da sauran hukumomin tsaron da abin ya shafa na gudanar da cikakken bincike akan dalilan da suka sabbaba afkuwar hatsarin.

Leave a Reply