Jami’an tsaro sun kama wata matashiya da ke kai wa ‘Bello Turji’ makamai
Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da kama wata matashiya da ke jigilar kai wa ‘yan bindiga makamai a Jihar Zamfara.
Sojojin Operation Fansan Yamma ne suka kama Shamsiyya Ahadu ‘yar shekara 25 a ranar Asabar 28 ga watan Disamba bayan sun samu bayanan sirri game da ita.
Sun kama ta ne tare da abokin aikinta Ahmed Hussaini a wani shingen bincike da ke kan hanyar Kware zuwa Badarawa a Ƙaramar Hukumar Shinkafi.
A sanarwar da Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar wanda shi ne mai magana da yawun rundunar ta musamman ta Operation Fansan Yamma, ya bayyana cewa an samu Shamsiyya da harsasai 764 da magazine shida wadda za a kai wa sansanin Bello Turji.
KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda sun kama wani ɗan Nijar da ake zargi da safarar makamai
“An kama ta bayan mun samu bayanan sirri kan hanyar da za ta bi ta Kware zuwa Badarawa a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara,” in ji sanarwar.
“Sakamakon bayanan da aka samu, sojojin Operation Fansan Yamma sun yi gaggawar saka shingen bincike domin kama wadda ake zargi. Duka waɗanda ake zargin na fuskantar bincike daga hukumomin da suka dace,” in ji sanarwar.
Sojojin Najeriya na yaƙi da da ‘yan ta’adda musamman a arewa maso yammaci da arewa maso gabashin ƙasar.
Ko a cikin watan nan na Disamba sai da hedikwatar tsaron ƙasar ta sanar da cewa sun kashe ‘yan ta’adda 8,034 kuma suka kama mutum 11,623 da ake zargi da ta’addanci tare da kuɓutar da mutum 6,376 da aka yi garkuwa da su daga watan Janairu zuwa watan Disambar 2024.