Ƙananan yara da yawa sun mutu a turmutsitsi a wajen bikin ƙarshen shekara

0
23
Ƙananan yara da yawa sun mutu a turmutsitsi a wajen bikin ƙarshen shekara

Ƙananan yara da yawa sun mutu a turmutsitsi a wajen bikin ƙarshen shekara

Mutane da dama, galibinsu ƙananan yara, sun rasa rayukansu a wani turmutsitsi da ya afku yayin bikin nuna al’adun ƙarshen shekara da aka shirya wa yara a makarantar Basorun High School da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Duk da cewa ba a bayyana yawan adadin mutanen da suka mutu ba, gwamnatin jihar ta tabbatar cewa mafi yawan waɗanda suka rasa rayukansu ƙananan yara ne.

Turmutsutsun ya faru ne a ranar Laraba, inda wasu kuma suka samu raunuka da ke buƙatar kulawar gaggawa.

KU KUMA KARANTA: Israila ta tagayyara ƙananan yara fiye da dubu 400 a Lebanon; UNICEF

An kai waɗanda lamarin ya shafa zuwa asibitoci mafi kusa a Ibadan domin kula da su.

A wata sanarwa da Prince Dotun Oyelade, kwamishinan yaɗa labaran jihar, ya fitar, ya bayyana cewa ba su da masaniya kan taron kafin afkuwar lamarin.

Ya kuma ce da sun bayar da goyon baya don tabbatar da tsaron taron da aka shirya wa yara.

Leave a Reply