‘Yansanda a Kano sun kama matasa 24 kan zargin faɗace-faɗace a unguwanni

0
24
'Yansanda a Kano sun kama matasa 24 kan zargin faɗace-faɗace a unguwanni

‘Yansanda a Kano sun kama matasa 24 kan zargin faɗace-faɗace a unguwanni

Daga Jamilu Lawan Yakasai

Rundunar ‘yansandan jihar Kano ta samu nasarar kama mutane 24, waɗanda dukkansu matasa ne ɗauke da muggan makamai bisa zarginsu da yin faɗa unguwanni.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yansandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar ta ce an samu nasarar kama matasan ne biyo bayan fadace-fadacen da ya faru tsakanin Kafar Mata, yakasai, Zango, Zage da kuma sauran maƙotan unguwanni, daga ranar 10 zuwa 12 ga watan Disamban 2024.

A ranar 13 zuwa 16 ga watan da muke ciki kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Salman Dogo Garba, ya tura dakarun ‘yansanda zuwa sassan wuraren da lamarin faru tare da bibiyar halin da ake ciki har aka samu nasarar cafke matsan da ake zargi ɗauke da mugan makamai.

KU KUMA KARANTA: ’Yansanda a Borno sun kama ɓarayi 2 da ƙwato wayoyi 25

Rundunar ‘yansandan ta bayar da nambobin ƙiran gaggawa.
– 08032419754
– 08123821575
– 09029292926.

Leave a Reply