Babu yadda Majalisa za ta yi wani abu da al’umman ƙasa ba su amince da shi ba – Sanata Akpabio 

0
26
Babu yadda Majalisa za ta yi wani abu da al'umman ƙasa ba su amince da shi ba - Sanata Akpabio 

Babu yadda Majalisa za ta yi wani abu da al’umman ƙasa ba su amince da shi ba – Sanata Akpabio

Majalisar Dattawa ta yi amai ta lashe inda ta ce ba ta soke yin aiki kan kudurin sake fasalin haraji da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kawo mata ba.

A zaman Majalisar na ƙarshen makon nan sai shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa Opeyemi Bamidele ya bayyana a zauren Majalisa cewa, babu inda Majalisar dattawa ta ce za ta dakatar da aiki akan ƙudurin, kasancewa ƙudurin daga ɓangaren gwamnati ya ke, saboda haka su ne kadai za su iya janye shi.

Opeyemi ya ce Majalisar ta mika Kudurin ga kwamitin kula da harkokin kuɗi domin ya yi bitar ƙudurin ɗaya bayan ɗaya har ya buɗe dandalin sauraron bahasin jama’a akai. Ya ce ba daidai ba ne a ce mun dakatar da aiki kan kudurin.

To amma Sanata Mai Wakiltan Bauchi ta Kudu, Shehu Umar Buba ya ce Sanatocin Jamiyyar APC da na Arewa baki daya sun yi taro inda suka yi matsaya cewa a dakatar da aiki akan kudurin har sai su da al’umansu da suke wakilta sun fahimci abinda ƙudurin ya ƙunsa tukuna.

Shehu ya ce suna ganin akwai lauje cikin nadi kan yadda wadanda suka kawo Kudurin suke hanzari akai, saboda haka idan za su yi adalci, ba za su amince ba har sai al’umma sun amince tukuna.

Shi ma dan Majalisa mai Wakiltan Karamar Hukumar Fagge ta Jihar Kano Mohammed Bello Shehu ya bada bayanin abinda ya sa suka janye aiki akan Kudurin dokar inda ya ce zazzafan ƙorafe kƙorafe da aka yi ta samu daga wurin al’umma musamman ma daga shiyar Arewa shi ne ya sa suka dakatar da aiki akan ƙudurin.

KU KUMA KARANTA: An dakatar da sabuwar dokar haraji a Najeriya

Mohammed ya ce idan mutum ya je wani shago a lagos ya sayo waya, ai lagos ce za ta amfana da harajin da aka ɗora a wayar, kuma idan mutum ya zo sayar da wayar a Kano dole ya dora riba akan wayar, da kuma wani harajin, shi ne ake cewa DOUBLE TAXATION a turanci, saboda haka an dora wa talaka haraji biyu kenan.

Mohammed ya ce su za su yi aiki akan dokar idan an bi sigar da su ‘yan Arewa suke so.

A ɓangaren Sanatocin Kudu kuma, tsohon Gwamnan mai wakiltan Jihar Bayelsa ta yamma Sanata Seriake Dickson yayi tsokaci kan batun dokar sauya fasalin harajin inda ya ce yana goyon bayan Kudurin dokar amma ya fi son a sake duba shi sosai, saboda kar a yi wa wasu jihohin choge.

Seriake ya ce idan kana Bayelsa kuma ka sayi simintin Dangote ko Bua daga jihar Kano, ya kamata harajin da aka dora kan kudin simintin nan ya je jihar Kano, ba wai Ofishin da ke Jihar Lagos ba.

Saboda haka, yana mai bada shawarar a sake duba ƙudurin dokar sosai saboda a yi wa kowa adalci.

Shi kuwa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya ce babu yadda Majalisar za ta yi wani abu da al’umman Ƙasa ba su amince da shi ba.

Saboda haka ya kafa Kwamiti na Musamman a ƙarƙashin shugaban marasa rinjaye Sanata Abba Moro domin haɗa gwiwa da Ofishin Shari’a na ƙasa saboda a tantance dokar kafin a dawo da ita ga Majalisar.

Wannan ƙudirin doka mai ƙunshe da ɓangarori huɗu ya yi watanni biyu a Majalisar Ƙasa inda aka yi ta mahawara akan sa.

Leave a Reply