Za mu tabbatar Majalisa ta yi watsi da dokar haraji – Tambuwal
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewar za su tabbatar ƙudirin canza fasalin dokokin haraji da gwamnatin tarayya ta kai a majalisar ƙasa bai kai labari ba.
Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa ya bayyana cewar dokokin da gwamnatin tarayya a ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ke son kakaɓawa jama’a ba su dace ba, don haka ba za su goyi bayan su ba.
Tsohon Gwamnan kuma jagoran jam’iyyar PDP a Sakkwato ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Shagari a yayin da yake ƙaddamar da tallafi ga waɗanda ambaliyar ruwa da hare – haren ta’addanci ya shafa a mazaɓarsa.
KU KUMA KARANTA: Sabon ƙudurin sabunta haraji a Najeriya, zai yiwa arewa naƙasu; Masharhanta
Tambuwal wanda ya shugabanci majalisar wakilai ta bakwai ya bayyana cewar al’umma suke wakilta a majalisa ba kan su ba kuma sun saurari ra’ayoyin jama’a waɗanda suka nuna rashin gamsuwa da dokokin don haka ba za su yi abin da zai cutar da al’ummarsu ba.
“Kun zaɓe mu ne don mu kare muradun ku da ra’ayoyin ku don haka muna tabbatar maku cewar da yardar Allah za mu kai karshen wannan matsalar ta hanyar watsi da wanɗanan dokokin da ke a gaban majalisar dattawa da majalisar wakilai.”