‘Yansanda a Katsina sun ceto fasinjoji 14 daga hannun ‘yan bindiga
Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina, ta dakile yunƙurin sace mutane a kan hanyar Magama zuwa Jibia.
‘Yan bindiga sun kai wa motocin haya guda biyu hari, inda suka yi ƙoƙarin sace fasinjoji.
Sai dai jami’an ‘yansanda daga Jibia sun isa wajen da a kan lokaci, inda suka yi musayar wuta da ‘yan bindigar, wanda hakan ya sa suka tsere.
‘Yansanda sun samu nasarar ceto mutum 14. Amma, mutum biyu daga cikin waɗanda aka ceto sun samu raunin harbin bindiga.
An garzaya da su asibiti don ba su kulawa, kuma rahotanni sun nuna cewa suna cikin koshin lafiya.
Kakakin Rundunar ‘Yansanda, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya yaba wa jami’an da suka nuna jaruntaka tare da ɗaukar matakin gaggawa.
KU KUMA KARANTA: ‘Yansanda sun kama wani ɗan Nijar da ake zargi da safarar makamai
Ya tabbatarwa da al’umma cewa ‘yansanda za su ci gaba da aiki tuƙuru don yaƙi da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaro.
Adejobi, ya kuma yi ƙira ga mazauna yankin da su haɗa kai da jami’an tsaro ta hanyar ba su bayanai kan duk wani motsi ko aikata laifi.
Ya ce haɗin kan al’umma yana da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da ‘yan bindiga da sauran miyagun ayyuka.