Gurfanar da baƙin haure kan zargin aikata laifuffukan Intanet ya ci tura

0
12
Gurfanar da baƙin haure kan zargin aikata laifuffukan Intanet ya ci tura

Gurfanar da baƙin haure kan zargin aikata laifuffukan Intanet ya ci tura

Gurfanar da waɗanda ake tuhumar a gaban kotu ya gamu da cikas sakamakon kura-kuran da aka samu wajen shigar da sunayen mutanen a kan takardar tuhuma da kuma batutuwan da suka shafi lauyan da zai wakilce su.

Mai Shari’a Ekerete Akpan na babbar kotun tarayya dake Abuja ya ba da umarnin adana wasu baƙin haure 109 da ake dangantawa da laifuffukan intanet da yin kutse ta na’ura da sauran laifuffukan dake barazana ga tsaron Najeriya a gidajen gyaran hali na Kuje dana Suleja har sai ranar da aka tsayar domin zaman kotun na gaba.

Mai Shari’a Akpan ya ba da umarnn ne biyo bayan bukatar da lauyan wadanda ake kara ya gabatar ta cewa wurin da ake tsare da mutanen a caji ofis din ‘yan sanda bai dace da dimbin wadanda ake tuhumar ba.

KU KUMA KARANTA:Ina godiya ga jaridar Neptune Prime – Husaina Mai Awara

Gurfanar da wadanda ake tuhumar a gaban kotu ya gamu da cikas sakamakon kurakuran da aka samu wajen shigar da sunayen mutanen a kan takardar tuhuma da kuma batutuwan da suka shafi lauyan da zai wakilce su.

Bayan da ya saurari hujjojin lauyoyin bangarorin dake cikin karar ne, alkalin kotun ya dage zamanta zuwa ranar 29 ga watan Nuwamban da muke ciki domin gurfanarwar.

Kafin tsaikon baya-bayan nan, an samu tsaiko wajen gurfanar da mutanen a ranar da aka ajiye domin sauraron karar saboda rashin lauyan da zai wakilci mutanen a kotu.

Leave a Reply