Muna ɗaukar mataki don magance rikicin manoma da makiyaya – Tinubu

0
12
Muna ɗaukar mataki don magance rikicin manoma da makiyaya - Tinubu

Muna ɗaukar mataki don magance rikicin manoma da makiyaya – Tinubu

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne lokacin da yake rattaba hannu kan takardar yarjejeniya tsakanin gwamnatin Najeriya da JBS S.A, daya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa nama a duniya.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa ta kawo karshen yawaitar rikicin manoma da makiyaya da ya yi sanadiyar salwantar rayuka da dama.

Tinubu yace sabon kudirinsa na janyo masu zuba jari a harkar kiwon dabbobi daga ciki da wajen kasar nan zai magance yawaitar rikicin manoma da makiyaya tare da kawar da fatara da yunwa daga Najeriya da kuma bunkasa cigaban tattalin arzikinta.

KU KUMA KARANTA:‘Yan Najeriya sun bayyana damuwa kan bashin da Tinubu ke shirin ciwo wa

Shugaba Tinuby ya bayyana hakan ne lokacin da yake rattaba hannu kan takardar yarjejeniya tsakanin gwamnatin najeriya da JBS S.A, daya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa nama a duniya.

Tinubu ya bukaci kamfanin ya yi nazarin dimbin albarkatun daya bayyana da damar zuba jarin dala bilyan 2.5 a harkar kiwo a Najeriya, musamman cin gajiyar dimbin al’ummar da take da shi, duba da kwarewar da kamfanin keda shi a fadin duniya wajen tabbatar da wadatar abinci.

Leave a Reply