Kama Mabarata a Najeriya: Wani babban lauya ya maka ministan Abuja a kotu

0
94
Kama Mabarata a Najeriya: Wani babban lauya ya maka ministan Abuja a kotu

Kama Mabarata a Najeriya: Wani babban lauya ya maka ministan Abuja a kotu

Babban Lauya a Najeriya Barista Abba Hikima ya maka Ministan Abuja Nyesom Wike a kotu, sakamakon kama Mabarata da masu ƙananan sana’o’i a birnin tarayya Abuja.

Abba Hikima ya kai ƙarar ne a babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ƙarar ta haɗa da Ministan Abuja da Gwamnatin Najeriya da Darakta Janar na DSS da kamu sufetan ƴan sandan Najeriya.

Hikima ya ce doka ta bawa kowa damar ya zauna duk inda yake so a Najeriya, indai ba zai saba wa dokokin kasar ba.

KU KUMA KARANTA: Ba za mu daina rusau a Abuja ba – Wike 

Hakan ya biyo bayan da jami’ai ke ci gaba da kama Mabarata a birnin Abuja.

Leave a Reply