Kotu ta soke tuhumar da ake yi wa mutanen da suka yi zanga-zanga

0
52
Kotu ta soke tuhumar da ake yi wa mutanen da suka yi zanga-zanga

Kotu ta soke tuhumar da ake yi wa mutanen da suka yi zanga-zanga

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta soke ƙarar da aka shigar a gabanta kan zargin da ake yi wa wasu ‘yan Najeriya na cin amanar ƙasa bayan sun gudanar da zanga-zanga game da tsadar rayuwa mai taken #EndBadGovernance a watan Agusta.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a Obiora Egwuatu, a ranar Talata ya soke ƙarar bayan M. D Abubakar, lauyan Antoni Janar na Nsjeriya ya shigar da buƙatar yin hakan.

Ya ɗauki matakin ne kwana guda bayan shugaba Bola Tinubu ya umarci kotu ta saki ƙananan yara da aka gurfanar a gabanta, waɗanda suke cikin mutanen da gwamnatin tarayyar ƙasar ta zarga da cin amanar kasa, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a ƙasar.

Kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa Antoni Janar na ƙasar, Lateef Fagbemi, damar janye ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar a gaban kotu ta hanyar karɓe lamarin daga hannun Babban Sufeton Rundunar ‘Yansanda.

KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin sakin ƙananan yaran da aka kama lokacin zanga-zanga

Daga nan ne Mai Shari’a Egwuatu ya soke ƙarar abin da ke nufin an wanke mutum 119 daga zargin da gwamnati ta yi musu na cin amanar ƙasa.

Ko da yake mutanen ba su bayyana a gaban kotun ba, alƙalin ya yi umarni a sake su daga gidan yari nan-take.

Leave a Reply