Kashi 6 cikin 10 na yara na fuskantar wani nau’i na cin zarafi – UNICEF

0
99
Kashi 6 cikin 10 na yara na fuskantar wani nau'i na cin zarafi - UNICEF

Kashi 6 cikin 10 na yara na fuskantar wani nau’i na cin zarafi – UNICEF

Hukumar kula da lamuran yara ta majalisar ɗinkin duniya, UNICEF ta yi gargaɗin cewa wani bincike da ta gudanar ya nuna yadda matsalar zarafin ƙananan yara a Najeriya ke ƙaruwa.

Jami’ar sashin bai wa yara kariya ce, Monica Aika, ta bayyana haka a yayin buɗe wani taron masu ruwa da tsaki da aka shirya domin kawo ƙarshen gallazawa ƙananan yara a Najeriya.

Jami’ar hukumar, Monica Aiki, ta bayyana cewa kusan kashi 6 cikin 10 na yara na fuskantar wani nau’i na cin zarafi, kuma kashi 5 cikin 100 ne kawai na waɗanda suka bayar da wani bayani ɗaya danganci aukuwar lamarin ke samun tallafi da kulawa.

A matsayin fargar jaji ga wannan binciken, Najeriya ta ɗauki matakai wajen ƙarfafa gwiwar waɗanda ke matuƙar ƙoƙari wajen kulawa da yaran da suka fuskanci matsalar da kuma kiyaye cin zarafinsu a nan gaba.

KU KUMA KARANTA: Rashin abinci mai gina jiki na barazana ga miliyoyin yara a Afrika.

Ta ƙara da cewa sun yi  ƙoƙari wajen tabbatuwar aiki cikin tsari da aiwatar da dokoki da kawar da ɗabi’un da ke ƙarfafa wariyar jinsi da kuma ayyuka masu cutarwa kamar kaciyar mata da auren yara tare da samar da ingantaccen yanayi, hakazalika da kuma tallafawa iyaye da kuma masu ba da kulawa.

A nata jawabin, lauyar gwamnatin tarayya kuma babbar sakatariya a ma’aikatar shari’a ta Najeriya, Beatrice Jeddy-Agba, wadda ta ba da misali da binciken da hukumar ƙidaya ta ƙasa ta gudanar tun farko, ta ce kawo ƙarshen cin zarafin ƙananan yara yana buƙatar a bi matakai daban-daban tare da samun haɗin kai.

Ita kuwa, daraktar hukumar kula da shari’ar manyan laifuka ACJRD a ma’aikatar shari’a ta kasar, Leticia Ayoola-Daniels cewa ta yi kasancewar taron share fage ne gabanin taron kolin duniya da za a yi a Bogota na ƙasar Colombia, zai bayar da damar duba irin ababen da suka kamata ayi wajen magance matsalar.

Leave a Reply